NDLEA ta kama gawurtaccen dilan miyagun kwayoyi da aka dade ana nema a Abia

NDLEA ta kama gawurtaccen dilan miyagun kwayoyi da aka dade ana nema a Abia

- Jami'an hukumar NDLEA sun damke gagarumin dilan miyagun kwayoyi da suka dade suna nema

- Chibuike Apolos ya shiga hannun jami'an ne a safiyar Laraba a wani samame da suka kai gidan dake Abia

- An kama shi da buhu sama da 100 na wiwi, sinkin hodar iblis da sauran kayan maye da yake siyarwa

Jami'an hukumar yaki da miyagun kwayoyi da fasa-kwabrinsu (NDLEA) ta kama wani matashi mai suna Chibuike Apolos, a kan zarginsa da zama gawurtaccen mai siyar da miyagun kwayoyin da ta dade tana nema a jihar Abia.

Femi Babafemi, kakakin hukumar, ya bayyana hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Laraba.

Babafemi yace an kama Apolos a ranar Laraba yayin wani samamen sassafe da jami'an suka kai maboyarsa dake yankin Isialangwa dake jihar. Sun same shi da sama da 100kg na miyagun kwayoyi.

Ya kara da cewa, wanda ake zargin babban mai rarraba miyagun kwayoyi ne ga masu siyarwa kuma tun a watan Fabrairu hukumar ke nemansa.

KU KARANTA: Jama'a sun tarwatse neman tsira bayan harbe-harbe ya cika hanyar Enugu-Abakaliki

NDLEA ta kama gawurtaccen dilan miyagun kwayoyi da aka dade ana nema a Abia
NDLEA ta kama gawurtaccen dilan miyagun kwayoyi da aka dade ana nema a Abia. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

KU KARANTA: Tunda na shiga aikin dan sanda, ban taba harbin kowa ba, Dan sandan da Gwamna ya karrama

"Bayan kama shi da aka yi a sa'o'in farko na ranar Laraba, gwamnatin jihar Abia tace zata rushe gidansa wanda ya zama maboyarsa," Babafemi yace.

"Hukumar, reshen jihar Abia tana nemansa tun daga watan Fabrairu. Cike da sa'a muka samu labarin ya karba wasu wiwi daga Edo.

“Duk da halin tsaron da yankin kudu maso gabas ke ciki, ballantana Abia, hukumar ta kai samamen inda ta kama Apolos.

“An kama shi da buhu goma na wiwi mai nauyin 100kg, hodar iblis mai nauyin 1.6g da sauran wasu miyagun kwayoyi.

Wanda ake zargin yana daya daga cikin masu rarraba miyagun kwayoyi a Abia ballantana yankin Isialangwa. Gwamnan jihar ya bada umarnin rushe gidan wanda aka kaman"

Buba Marwa, shugaban hukumar NDLEA, ya jinjinawa hukumar reshen jihar Abia a kan wannan kamen.

A wani labari na daban, Usman Baba, sabon mukaddashin shugaban 'yan sandan Najeriya, ya janye dukkan manyan jam'ian 'yan sanda dake hukumar yaki da rashawa da hana yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa.

Kamar yadda jaridar The Cable ta wallafa, umarnin na kunshe ne a wata wasika mai kwanan wata 15 ga watan Afirilun 2021 wacce aka aiketa ga Abdularasheed Bawa, shugaban EFCC.

A wasikar wacce Idowu Owohunwa yasa hannu, 'yan sanda daga mukamin CSP ana bukatar hukumar EFCC ta sake su kuma su kai kansu hdekwatar 'yan sanda a ranar Laraba da karfe 10 na safe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel