IGP ya janye dukkan manyan jami'an 'yan sanda daga EFCC

IGP ya janye dukkan manyan jami'an 'yan sanda daga EFCC

- Mukaddashin shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya ya bukaci dukkan manyan jami'an 'yan sanda da su bar hukumar EFCC

- A wasikar da ya aikewa hukumar mai kwanan wata 15 ga Afirilu, yace duk dan sandan da ya kai mukami CSP ya bar hukumar

- Manyan bincike a hukumar EFCC duk jami'an 'yan sanda ke yi, hasalima dukkan shugabannin hukumar daga 'yan sanda ake nadawa banda Bawa

Usman Baba, sabon mukaddashin shugaban 'yan sandan Najeriya, ya janye dukkan manyan jam'ian 'yan sanda dake hukumar yaki da rashawa da hana yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa.

Kamar yadda jaridar The Cable ta wallafa, umarnin na kunshe ne a wata wasika mai kwanan wata 15 ga watan Afirilun 2021 wacce aka aiketa ga Abdularasheed Bawa, shugaban EFCC.

A wasikar wacce Idowu Owohunwa yasa hannu, 'yan sanda daga mukamin CSP ana bukatar hukumar EFCC ta sake su kuma su kai kansu hdekwatar 'yan sanda a ranar Laraba da karfe 10 na safe.

KU KARANTA: Bakatsine ya yanka rago, ya shirya kayatacciyar liyafar dawowar Buhari daga London

IGP ya janye dukkan manyan jami'an 'yan sanda daga EFCC
IGP ya janye dukkan manyan jami'an 'yan sanda daga EFCC. Hoto daga @TheCableng
Asali: Twitter

KU KARANTA: Jihohi 8 da aka kama 'yan kasuwa 400 masu daukar nauyin Boko Haram da 'yan bindiga

Hukumar 'yan sandan ce ta sanar da wannan hukuncin. Wasikar ta ce: "Na rubuto domin in miko gaisuwar sifeta janar na 'yan sanda tare da sanar da shugaban hukumar EFCC akan janye dukkan manyan 'yan sanda da mukaminsu ya kai CSP zuwa sama daga hukumar."

"Wannan hukuncin ya fito daga hukumar. Ana bukatar ku bada umarnin sakin dukkan jami'an da abun ya shafa kuma su kai kansu hedkwatar 'yan sanda a ranar Laraba, 21 ga watan Afirilun 2021."

Wannan umarnin yana zuwa ne kasa da makonni uku da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Baba a matsayin mukaddashin shugaban 'yan sandan.

Cigaban na zuwa ne bayan kwanaki kadan da Baba ya bukaci rushe wani sashi na 'yan sandan Legas da Fatakwal.

Wilson Uwujaren, kakakin hukumar EFCC, bai samu yin martani ba a kan wannan cigaban bayan an tura masa sakon kar ta kwana.

Duk da hukumar tana da nata gogaggun ma'aikatan, manyan ayyukan bincike na hukumar duk jami'an 'yan sanda ke yin su.

Tsoffin shugabannin hukumar duk ana zabosu ne daga cikin 'yan sanda amma kuma Bawa ne mutum na farko da aka nada shugabancin hukumar wanda ba dan sanda ba.

A wani labari na daban, masarautar Kano ta musanta siyar da filayen Gandun Sarki wadanda yasa hukumar yaki da rashawa ta jihar kano take tuhumar Sarki Aminu Bayero da shi.

Daily Trust ta ruwaito cewa, hukumar yaki da rashawan tana bincikar masarautar akan zargin siyar da filaye har kadada 22 dake Gandun Sarki a Dorayi Karama ta karamar hukumae Gwale dake jihar Kano tare da waskar da kudin zuwa aljihunsu.

Takardun karar da wani wanda ya siya filin, Alhaji Yusuf Aliyu ya shigar, ta bukaci kotun da ta dakatar da shugaban hukumar daga hana su aikin ginin da suka fara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel