Tunda na shiga aikin dan sanda, ban taba harbin kowa ba, Dan sandan da Gwamna ya karrama

Tunda na shiga aikin dan sanda, ban taba harbin kowa ba, Dan sandan da Gwamna ya karrama

- Dan sanda da mai abun hawa yaci zarafi, ASP Sunday Erhabor yace bai taba harin kowa ba ashekaru 29 da yayi yana aiki

- Dan sandan mai hakuri, yayi suna ne bayan wani bidiyonsa da ya yadu inda mai abun hawa ya ci masa mutunci a kan titi duk da yana da bindiga

- Erhabor yace yana fuskantar cin zarafi daga jama'a amma bai taba tunanin amfani da bindigarsa ba a cikin wannan hali

Sunday Erhabor, dan sanda mai mukamin ASP, wanda wani mai abun hawa yaci zarafi a jihar Legas, yace bai taba harbin kowa ba tunda ya shiga aikin dan sanda a shekarar 1992.

Bidiyon yadda wani mutum da 'yan sandan runduna ta musamman suka tsayar, amma ya ci zarafin 'yan sandan ya fada kafafen sada zumuntar zamani.

An ga direban mai suna Victor Ebhomenyen, yana ture Erhabor, wanda ke dauke da bindiga kirar AK-47, a kirji yayin da yake yunkurin kai shi kasa, TheCable ta ruwaito.

KU KARANTA: Ta fasu: Sunayen 'yan canji a Najeriya da aka kama suna turawa 'yan Boko Haram kudi

Tunda na shiga aikin dan sanda, ban taba harbin kowa ba, Dan sandan da Gwamna ya karrama
Tunda na shiga aikin dan sanda, ban taba harbin kowa ba, Dan sandan da Gwamna ya karrama. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

KU KARANTA: Bakatsine ya yanka rago, ya shirya kayatacciyar liyafar dawowar Buhari daga London

A wata tattaunawa da aka yi da Erhabor, yace yana fuskantar tsageranci daga jama'a amma bai taba tunanin yin amfani da bindigarsa ba a irin wadannan lokutan.

"Na shiga aikin dan sanda a ranar 1 ga watan Yunin 1992. Ina da sauran shekaru 5 kafin in yi murabus. Ubangiji ne yake taimakona a wannan aikin," yace.

"Wani abu ya faru a lokacin da nake FESTAC. Ina aikin duba ababen hawa a kan hanyar Okota. Na tsayar da mota dauke da miji da matsa. Matar ta sauko, ta wanke ni da mari.

"Nayi shiru yayin da take tambaya a kan mene na tsaresu. Kai tsaye na nufi wurin mutumin inda na tambayeshi ko shine mijin matar, yace eh.

"Sai na sanar dashi cewa matar shi ta mare ni, amma ina son ta mare shi idan har ya cika namiji. Wannan na daya daga cikin arangamata da jama'a.

"Na fuskanci cin zarafi daban-daban, amma na kan kwantar da hankalina kuma bana sauke fushina a kan jama'a," ya bada labari.

A wani labari na daban, a kalla 'yan kasuwa 400 ne aka kama sakamakon zarginsu da ake yi da daukar nauyin 'yan ta'addan Boko Haram da 'yan bindiga.

Sama da shekaru 10, an kasa samun bayanai masu inganci a kan yadda mayakan ta'addanci ke samun kudi.

Kamar yadda aka gano, an kama wasu 'yan kasuwa sakamakon binciken hukumomin DIA tare da hadin guiwar DSS, NFIU da CBN.

Asali: Legit.ng

Online view pixel