Jama'a sun tarwatse neman tsira bayan harbe-harbe ya cika hanyar Enugu-Abakaliki

Jama'a sun tarwatse neman tsira bayan harbe-harbe ya cika hanyar Enugu-Abakaliki

- A halin yanzu tashin hankula tare da neman hanyar tsira ya cika babbar hanyar Enugu zuwa Abakaliki

- Masu ababen hawa a halin yanzu sun tsaya cak inda wasu ke neman mafaka sakamakon harbe-harben dake tashi

- Rundunar 'yan sandan jihar Ebonyi ta tabbatar da aukuwar lamarin kuma tace jami'ai suna kan hanyar zuwa wurin

Rahotanni daga jaridar The Nation sun nuna cewa ababen hawa da fasinjoji dake kan babbar hanyar Enugu zuwa Abakaliki sun tsaya sakamakon harbe-harben dake tashi a yankin Ezilo.

Kamar yadda tahotanni suna nuna, har yanzu ba a san abinda ya kawo harbe-harben ba.

An gano cewa, an kashe wasu mutum biyu a sabon rikicin iyaka da aka yi tsakanin yankunan Ezilo da Iyionu dake karamar hukumar Ishielu ta jihar.

KU KARANTA: Masarautar Kano ta magantu a kan zarginta da ake yi da siyar da Gandun Sarki

Jama'a sun tarwatse neman tsira bayan harbe-harbe ya cika hanyar Enugu-Abakaliki
Jama'a sun tarwatse neman tsira bayan harbe-harbe ya cika hanyar Enugu-Abakaliki. Hoto daga @Thenation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Bakatsine ya yanka rago, ya shirya kayatacciyar liyafar dawowar Buhari daga London

Ba a tabbatar da cewa ko harbe-harben yana da alaka da rikicin iyakar da ake yi ba.

Wani fasinja mai suna Afam Cyprian, wanda ke kan hanyarsa ta zuwa Enugu, yace: "Matafiya da yawa na neman wata hanya. Wasu sun koma kan hanyar Afikpo. Ina neman hanyar komawa Abakaliki."

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan, Loveth Odah, ta tabbatar da aukuwar lamarin inda tace kwamishinan 'yan sandan jihar Ebonyi, Aliyu Garba, ya tura jami'an sintiri domin tabbatar da zaman lafiya tare da buda hanyar.

Amma kuma tace harbe-harben basu da alaka da rikicin yankin da aka fara tunda dama basu kusa da babbar hanya.

A wani labari na daban, a watan da ya gabata ne Malam Garba Shehu, babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa akan yada labarai, yace gwamnatin tarayya ta kama wasu 'yan canji da ke turawa 'yan Boko Haram kudi.

Ya ce wasu 'yan Najeriya dake zama a daular larabawa (UAE) sune ke aiki da 'yan canjin wurin turawa 'yan ta'addan kudi. "'Yan canji ne ke turawa 'yan ta'adda kudi. Tuni muka fara aiki da UAE. An samu nasarar kama wasu 'yan Najeriya dake turawa 'yan ta'addan Boko Haram kudi kuma wannan na faruwa har a cikin gida.

"Ina sanar daku, a wannan lokacin mun kammala bincike kuma 'yan Najeriya zasu sha mamaki," Shehu yace.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel