Jam'iyyar PDP da dakatar da Sanata Hayatu Gwarzo a Kano

Jam'iyyar PDP da dakatar da Sanata Hayatu Gwarzo a Kano

- Jam'iyyar PDP ta dakatar da Sanata Bello Hayatu Gwarzo na tsawon watanni shida

- An dakatar da Gwarzo ne kan zargin yi wa jam'iyya zagon kasa da kin amsa gayyatar jam'iyya ya kare kansa

- Gwarzo na daga cikin wadanda suka yi takarar neman kujerar shugabancin mataimakin shugaban jam'iyya na kasa shiyar Arewa maso Yamma a zaben da aka yi a Kaduna

Jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, a mazabar Gwarzo a jihar Kano, a ranar Laraba ta dakatar da tsohon dan majalisa mai wakiltar Kano ta Arewa a majalisar tarayya, Sanata Bello Hayatu Gwarzo.

Dakatarwar ba za ta rasa nasaba zarginsa da hada kai tsagin Ambasada Aminu Wali na jam'iyyar ta PDP ba kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Jam'iyyar PDP da dakatar da Sanata Hayatu Gwarzo a Kano
Jam'iyyar PDP da dakatar da Sanata Hayatu Gwarzo a Kano. Hoto: @MobilePunch

DUBA WANNAN: Ali Sarkin Mota: Allah ya yi wa direban Sardauna rasuwa

Idan za a iya tunawa, tsagin ta dakatar da tsohon gwamna Rabiu Musa Kwankwaso bayan zarginsa da hannu cikin rura rikicin da ya faru yayin taron jam'iyyar na Arewa maso Yamma da aka yi makon da ta gabata a Kaduna.

Shugaban PDP na mazabar Gwarzo, Idris Danbaba da sakatarensa, Sanusi Ibrahim a wata wasika da suka yi tarayya wurin rattaba hannu sun ce jam'iyyar ta dakatar da Sanata Bello Hayatu Gwarzo kan zarginsa da yi zagon kasa.

Sun kara da cewa kwamitin ladabtarwa ne ta bada shawarar dakatar da shi domin ya ki bayyana a gabanta ya kare kansa bisa zargin da ake masa.

KU KARANTA: Kotun shari'a ta raba aure a Zamfara saboda tsabar girman mazakutar miji

Wasikar ta ce an dakatar da shi 'saboda kin bayyana gaban kwamitin ladabtarwa, hakan kuma ya saba wa sashi na 58(1) na kudin tsarin PDP na 2017 da aka yi wa kwaskwarima'.

Dakatarwar da aka masa na watanni shida zai fara aiki nan take a cewar wasikar.

Sanata Gwarzo na daga cikin wadanda suka yi takarar neman kujerar mataimakin shugaban jam'iyyar na kasa shiyar Arewa maso Yamma da aka yi a Kaduna.

A wani labarin daban kun ji cewa 'yan sanda a jihar Kano sun ceto wata yarinya mai shekaru 15, Aisha Jibrin, da iyayenta suka kulle ta a daki tsawon shekaru 10 a Darerewa Quaters a karamar hukumar Fagge ta jihar Kano.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan Kano, Abdullahi Kiyawa cikin sanarwar da ya fitar a ranar Talata ya ce mahaifiyarta Rabi Muhammad tana hannunsu amma mahaifinta ya tsere.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan Kano, Abdullahi Kiyawa cikin sanarwar da ya fitar a ranar Talata ya ce mahaifiyarta Rabi Muhammad tana hannunsu amma mahaifinta ya tsere.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: