Jiya ba yau ba: Bullar rasiɗin sayen mota ƙirar 'Beetle' kan Naira 3,908 ya jawo cece kuce
- Wani dan Najeriya mai suna Ayo Ojeniyi ya haddasa cece kuce a shafukan sada zumunta bayan ya wallafa hoton wata motar Beetle da aka siyar akan N3,908.40
- Ya tambayi masu amfani da shafukan sada zumunta me zasu iya siya da irin wannan kudi a yau kuma da yawa sun bayyana ra'ayinsu
- Wasu daga cikin wadanda suka mayar da martanin sun ce mutane da yawa ba za su iya siyan motar ba a lokacin saboda mafi karancin albashin shi ne N120
Wani dan Najeriya, Ayo Ojeniyi, ya tunawa mutane zamanin baya bayan ya wallafa hoton wata mota kirar Beetle da aka sayar akan N3,908.40 a shekarar 1982.
Ojeniyi ya kuma wallafa hoton rasiɗin da aka siya motar sannan kuma ya tambayi mutane game da abunda za su iya siya da irin wannan kudin a yau.
KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun sake kai hari wani sansanin sojoji a jihar Neja
Da yake mai da martani ga hoton, wani mai amfani da Facebook mai suna Aliyu Hamagam ya ce mafi karancin albashi a 1982 shi ne N120, yana mai cewa motar Beetle tana da tsada a can baya.
A cikin kalmominsa:
"A shekarar 1982, mafi karancin albashin kasa ya kasance N120 kawai. Don haka zaka iya fahimtar abin da ake nufi da mutum ya tara kimanin N4000 na motar Beetle."
Wale Keshinro ya rubuta:
"Duk da cewa motar VW beatles ya kasance a kan N3908, amma iyalai nawa ne suka mallaki motoci a wancan zamanin sabanin yanzu. 6 daga cikin iyalai 10 a zamanin nan suna samar da masu motoci da yawa."
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun kai hari ofishin yan sandan Enugu, an kashe jami’ai uku
James Omeiza
"Mutane nawa ne zasu iya siyan volkswagen a cikin 1982? Amma a yau, wannan shine abin da matsakaicin ma'aikaci ke samu a wurin gini kowace rana.
"Akwai masu arziki a yau fiye da waɗanda muke da su a 1982."
A wani labarin, wasu ma'aurata 'yan Najeriya da aka ambata da suna Mista da Misis Ogeah suna murnar zuwan ‘yan ukunsu bayan shekaru 11 da aure da kuma bari da dama.
Wata 'yar uwarsu, Evelyn Odume, wacce ta ba da wannan labarin mai ban mamaki a ranar Lahadi, 11 ga Afrilu, ta bayyana cewa Allah ya ba shaidan kunya, Yabaleft ta ruwaito.
Shafin Twitter @Naija_PR ma ya yada labarin mai dadi a dandalin sada zumunta.
Asali: Legit.ng