Yanzu-Yanzu: An bindige wani makiyayi Fulani har lahira yayin da ya ke kiwon shanunsa a Ondo

Yanzu-Yanzu: An bindige wani makiyayi Fulani har lahira yayin da ya ke kiwon shanunsa a Ondo

- An kama wani mafarauci ya bindige makiyayi a cikin dajin Ifira Akoko a jihar Ondo

- Bala Umar, Sarkin Hausawa da Fulani na yankin ya tabbatar da afkuwar lamarin

- Bala ya yi kira ga Fulani su kwantar da hankalinsu domin ya san jami'an tsaro za su yi adalci

An bindige wani makiyayi Fulani, Muhammed Maikudi, a dajin Ifira Akoko da ke karamar hukumar Akoko ta Kudu na jihar Ondo, Daily Trust ta ruwaito.

Rahotani sun ce wani mafarauci mai suna Seyi Sansare ne ya kashe Maikudi a lokacin da ya ke kiwo tare da shanunsa a dajin na Ifira.

Yanzu-Yanzu: Mafarauci ya bindige makiyayi Fulani har lahira a Ondo
Yanzu-Yanzu: Mafarauci ya bindige makiyayi Fulani har lahira a Ondo. Hoto: @thecableng
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Ali Sarkin Mota: Allah ya yi wa direban Sardauna rasuwa

A halin yanzu ba a san ko an samu rashin jituwa tsakaninsu ba kafin ya harbe shi.

An gano cewa jami'an tsaron Amoketun na jihar da yan sanda sun dauki gawar mamacin sun kai asibitin gwamnati da ke karamar hukumar.

Jami'an tsaron sun kuma kama Sansare daga inda ya buya sun tafi da shi ofishinsu.

Shugaban Hausawa da Fulani na jihar, Bala Umar ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce binciken da aka fara ya nuna cewa mafaraucin ya bi sahun makiyayin ne har dajin sannan ya harbe shi.

KU KARANTA: Kotun shari'a ta raba aure a Zamfara saboda tsabar girman mazakutar miji

Sai dai ya yi kira ga Fulani da ke yankin su kwantar da hankulansu kuma kada su dauki doka a hannunsu.

"An tafi da wanda ake zargin hedkwatan yan sanda a Akure domin bincike. Muna kira ga mutanen mu su kwantar da hankulansu domin mun san gwamnati da jami'an tsaro za su yi adalci," in ji Bala.

Kakakin yan sandan jihar, Tee Leo Ikoro ya ce kawo yanzu ba a masa bayani kan afkuwar lamarin ba.

A wani labarin daban kun ji cewa 'yan sanda a jihar Kano sun ceto wata yarinya mai shekaru 15, Aisha Jibrin, da iyayenta suka kulle ta a daki tsawon shekaru 10 a Darerewa Quaters a karamar hukumar Fagge ta jihar Kano.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan Kano, Abdullahi Kiyawa cikin sanarwar da ya fitar a ranar Talata ya ce mahaifiyarta Rabi Muhammad tana hannunsu amma mahaifinta ya tsere.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan Kano, Abdullahi Kiyawa cikin sanarwar da ya fitar a ranar Talata ya ce mahaifiyarta Rabi Muhammad tana hannunsu amma mahaifinta ya tsere.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel