Ku kwantar da hankulan ku, Zamu tabbatar ba'a ƙara farashin litar man fetur ba, inji jam'iyyar APC

Ku kwantar da hankulan ku, Zamu tabbatar ba'a ƙara farashin litar man fetur ba, inji jam'iyyar APC

- Jam'iyyar APC mai mulki tace zata yi duk me yuwuwa wajen ganin ba'a ƙara farashin litar man fetur ba

- Sakataren kwamitin riƙo na jam'iyyar ne ya bayyana haka a wani taro da aka shirya a hedkwatar APC dake Abuja, domin bayyana nasarorin da gwamnatin Buhari ta samu

- Ya kuma ƙara da cewa abinda uwar jam'iyyar ta saka a gaba shine wayar da kan mutane su fito a dama dasu ta hanyar tsayawa takara a dukkan muƙaman da ake dasu a ƙasar nan

Jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar nan ta tabbatar da cewa ba zata bari a ƙara farashin litar man fetur nan kusa ba kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

Sakataren kwamitin riƙo na jami'iyyar, Sen. John Akpanudoedehe, shine ya bada wannan tabbacin ranar Talata a babban birnin tarayya Abuja.

KARANTA ANAN: Watan Ramadan: Mazauna Kano sun koka da tashin gwauron zabi da farashin ƙanƙara yayi a watan Azumi

Sakataren yayi wannan jawabi ne a wani taro da kwararrun yan jam'iyyar suka shirya a hedkwatar APC dake Abuja domin bayyana irin nasarorin da gwamnatin shugaba Buhari ta samu.

Akpanudoedehe, wanda ya wakilci shugaban kwamitin riƙo, Mai Mala Buni, a wajen taron, ya godema waɗanda suka shirya taron bisa ƙoƙarinsu na ƙara haskaka ma yan Najeriya irin nasarorin da gwamnatin ta samu.

Yace: "Wani abu da muka samu nasara akanshi shine farashin litar man fetur, APC bata yarda da ƙarin ba. munce har yanzun lokaci bai yi ba, wannan shine matsayar mu kuma gwamnati ta saurare mu."

Ya kuma tabbatar ma da ƙungiyar kwararrun waɗanda suka shirya taron cewa uwar jam'iyyar zata cigaba da haɗa kai dasu, ya ƙara da cewa shugaba Buhari yana da saukin kai wajen sauraren koken mutane.

Ku kwantar da hankulan ku, Zamu tabbatar ba'a ƙara farashin litar man fetur ba, inji jam'iyyar APC
Ku kwantar da hankulan ku, Zamu tabbatar ba'a ƙara farashin litar man fetur ba, inji jam'iyyar APC Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Sakataren ya cigaba da cewa:

"Duk wani abu da aka kai ma shugaba Buhari kokensa, ya riga da yasani, da zaran ka kai mishi koken wani abu zakaga ya ɗauki abun da matuƙar muhimmanci."

KARANTA ANAN: Wata Mata ta mare ni a gaban mijinta bance komai ba, ɗan sandan da gwamnan Lagos ya karrama

"A yanzun muna kokarin wayar da kan mutane ne domin su nemi takarar muƙamai a kowanne mataki a Najeriya, a wannan lokacin idan baka samu nasara ba to ba zamu barka hakanan ba."

"Ya zama wajibi ku fito takara, mata su fito takara, nakasassu da kwararrun matasa suma su fito a dama da su."

Akpanudoedehe ya ƙara da cewa kowa yasa a ransa cewa, shugaban kwamitin riƙo, Mai Mala Buni, mutum ne mai sauraran jama'a kuma duk abinda yasan zai zaburar daku to zai yishi ba tare da fargaba ba.

"Maganan nan da nike yi daku, mutane na amsar rance don rage raɗaɗin da annobar COVID19 ta haifar, kuma suna amfana da wasu tsare-tsaren da gwamnati ta fito dasu." injishi

A wani labarin kuma Rundunar Yan sanda ta Kuɓutar da yara ƙanana 19 da wasu mata 6 da ake ƙoƙarin safararsu

Rundunar yan sanda reshen jihar Edo ta kuɓutar da mutane 26 a jihar waɗanda akayi kokarin safarar su.

Hukumar tace waɗanda ta kuɓutar ɗin sun haɗa da ƙananan yara 19, da kuma matashiya ɗaya, sai kuma iyaye mata su shida.

Asali: Legit.ng

Online view pixel