Watan Ramadan: Mazauna Kano sun koka da tashin gwauron zabi da farashin ƙanƙara yayi a watan Azumi

Watan Ramadan: Mazauna Kano sun koka da tashin gwauron zabi da farashin ƙanƙara yayi a watan Azumi

- Mazauna garin Kano sun koka matuƙa da tashin gwauron zabi da farashin ƙanƙara yayi duk kuwa da shigowar watan Azumin Ramadan

- Mutane da yawa sunce farashin ƙanƙarar ya ƙaru sama da kashi 100%, domin ƙanƙarar da ake siyarwa N100 kafin azumi yanzun ta koma N250

- Sai dai dillalanta sun nuna cewa su kansu basajin daɗin tashin farashin amma ba yadda suka iya ne saboda yanzun basu samun wutar lantarki, dole sai dai su yi amfani da Man fetur ko Gas

Mazauna cikin garin Kano sun koka kan ƙarin farashin ƙanƙara da kashi 100% saboda yanayin zafi da aka shiga makonni kaɗan da suka gabata da kuma watan Ramadan.

Rahotanni sun nuna cewa masu sana'ar siyar da ƙanƙara sun mamaye hanyoyi a kwaryar birnin Kano suna gudanar da kasuwancinsu yadda suka ga dama.

KARANTA ANAN: Kwanaki tara bamu samu wanda ya mutu sakamakon COVID-19 ba, inji hukumar NCDC

Yayin da mazauna garin ke bin layi don siyan ƙanƙarar a farashin da masu siyarwan suka ga dama.

Da yawan mutane sunyi ƙorafin cewa suna kashe kuɗin da suka kai naira N500 kullum wajen siyan ƙanƙara saboda yanayin zafi da yake ƙara tsananta a birnin.

A cewar wasu masu siyan ƙanƙarar, ƙanƙarar da ake siyarwa N100 kafin watan Ramadan yanzun ta koma N250, wacce ake siyarwa N40 ta koma N100.

Nazir Sani, wani.mazaunin Ɗandinshe, yace bazai iya cigaba da ɗaukar wannan tashin farashin ba matuƙar aka cigaba da tafiya a haka.

Halima Abdullahi, wata mahifiyar 'yaya huɗu, tace duk da amfani da kankarar ya zama wajibi saboda yanayin zafin da aka shiga, ya kamata masu siyar da ita su duba yanayin tattalin arziƙin da ake ciki domin wasu mutanen ma suna fama ne da abincin da zasu ci.

Halima tace: "Muna cikin watan azumin Ramadana, tsammanin mu irin waɗannan abubuwa zasu ƙara sakkowa ne, amma masu siyar da ita suna amfani da wannan damar domin su yi kuɗi."

"A wajena ya zama wajibi na siya ko nawa suka ce, saboda bazan iya jure rashin ƙanƙara ba a cikin wannan yanayin na zafi da muke ciki."

Watan Ramadan: Mazauna Kano sun koka da tashin gwauron zabi da farashin ƙanƙara yayi a watan Azumi
Watan Ramadan: Mazauna Kano sun koka da tashin gwauron zabi da farashin ƙanƙara yayi a watan Azumi Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Lokacin da wakilan Dailytrust suka ziyarci ASADA, babbar kasuwar siyarda ƙanƙara dake hanyar Katsina wacce akafi sani da 'Gidan ƙanƙara', Sun gano cewa mutane na zuwa ne da ɗan mazubinsu su siya.

Amma manyan masu dillancin ƙanƙarar na zuwa ne da ƙananan motocin ɗaukar kaya da kuma keke nafef domin su ɗauki ƙanƙarar zuwa wani wuri mai nisa.

Aminu Lawan, wanda ya zanta da wakilin jaridar, yace basu da wani zaɓi sai dai su sayi ƙanƙarar a duk farashin da aka mata tunda idan sunkai ma mutane zasu siya.

KARANTA ANAN: Sheikh Pantami ya bayyana wata babbar Nasarar da gwamnatin tarayya ta samu a ɓangaren Fasahar Zamani

Aminu yace: "Mutane na zargin mu da tada farashin ƙanƙara, amma maganar gaskiya shine muna siyar da ita ne yadda muka siya kuma bamu da hannu a ƙarin farashin."

"Manyan masu samar da ita sun yi ƙorafin basu samun wuta yadda yakamata, dole tasa suke amfani da gas, wanda shine dalilin da yasa suka ƙara farashin."

Ɗaya daga cikin dilolin ƙanƙarar, wanda yake da shagon ƙanƙara a kasuwar, Abba Dauda, yace su kansu basa jin daɗin ƙarin farashin, amma saboda rashin wutar lantarki suna kashe kimanin N70,000 wajen siyan man gas kullum.

"In banda muna watan azumi, ba zamu yi amfani da injinan mu ba saboda wannan lokacin babu yawan bukatar ƙanƙara sosai, amma saboda shigowar watan yasa dole mu siya man gas ɗin domin mu samar ma mutane da ƙanƙara." inji Abba.

Mataimakin shugaban kasuwar ASAD, Alhaji Shamsudden Aliyu, ya ce suna aiki kafaɗa-da-kafaɗa da KEDCO domin warware matsalar ƙarancin wutar lantarkin. Ya kuma yi alaƙawarin farashin zai sakko nan bada jimawa ba.

Da aka tuntuɓi kakakin hukumar KEDCO, ya bayyana cewa rashin wutar ya wuce sanin hukumar su, amma yace hukumar rarraba wutar (TCN) ta riga ta yi jawabi kan abinda ya haddasa rashin samun wutar.

A wani labarin kuma An Kama fursunoni tara cikin waɗanda suka gudu daga gidan yarin Owerri a kasar Ghana

Hukumar yan sandan ƙasar Ghana ta kama tara daga cikin fursunonin da suka gudu daga gidan yari a Najeriya.

Yan sandan sun ce sun kama waɗanda ake zargin ne bayan samun bayanai akansu, kuma suka ɗana musu tarko.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262