Ofishin hukumar INEC ya kama ci da wuta a Kano, ana binciken abin da ya jawo gobarar

Ofishin hukumar INEC ya kama ci da wuta a Kano, ana binciken abin da ya jawo gobarar

- INEC ta ce ta na binciken abin da ya jawo wuta ta kona ofishin DPC a Kano

- Festus Okoye ya ce hukumar ta rasa wasu na’urori da kayan aiki a gobarar

- Ma’aikatan gwamnatin tarayya da ke kashe wuta su ka yi maganin gobarar

Hukumar da ke gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta, INEC, ta fara gudanar da bincike a game da abin da ya jawo gobara a wani ofishinta a Kano.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa wani dakin ajiye bayanai na hukumar ne ya kama da wuta.

Babban kwamishinan INEC kuma shugaban sashen yada labarai da wayar da kan masu zabe na kasa, Festus Okoye ya sanar da wannan a ranar Talata.

KU KARANTA: Bayan rikici ya barke a zaben PDP a Kaduna, an nada shugabannin riko

Kara karanta wannan

Wasu Shugabannin PDP na Neman Tada Rikici, Sun ce An Ware Su a Yakin Zaben Atiku

Da yake jawabi a Abuja, Festus Okoye ya ce babban kwamishinan zabe (REC) na jihar Kano, Farfesa Riskuwa Shehu ya sanar da auku war gobarar.

Kamar yadda Farfesa Riskuwa Shehu ya sanar da hedikwatar INEC jiya, wannan wuta ta ci ofishin tattara bayanai na hukumar wanda ake kira DPC.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Festus Okoye yake cewa gobarar ta barke ne da kimanin karfe 10:15 na safe, ta ci ofishin DPC kafin ma’aikatan kwana-kwana su iya kai ga kawo masu dauki.

“Ma’aikatan sun yi kokarin ganin sun kashe gobarar ta hanyar amfani da kayan kashe wuta, amma abin ya ci karfinsu, sai da 'yan kwana-kwana su ka zo.”

KU KARANTA: Kudin da ke shiga lalitar mu ya ragu – Zainab Ahmed

Ofishin hukumar INEC ya kama ci da wuta a Kano, ana binciken abin da ya jawo gobarar
Jami'in hukumar INEC, Festus Okoye
Asali: Twitter

“Daga cikin kayan da su ka kone akwai na’urar buga katin zabe, manyan na’urorin buga takardu na Laser Jet Printers da kayan aiki na Dell da Blade Servers.”

Kara karanta wannan

Gwamnati Ta Fadawa MTN, Glo, Airtel Su Dakata da Karin Farashin Da Suka Yi a Boye

Sauran kayan da aka rasa sun hada da manyan gafaka da kanana (DeskTop da Laptop) wanda ake amfani da su wajen horas da mutane da na’urar bada wuta.

A jawabinsa, Okoye ya ce akwai inda aka adana duka bayanan da aka rasa. Kwamishinan na INEC ya ce wannan gobarar ba ta jawo an rasa bayanai ba.

Kwanakin baya aka ji tsohon kwamishinan ayyuka na Kano ya na cewa duk da ilmin gwamna Abdullahi Ganduje, tantiran jahilai su ke rike da madafan iko.

Sanannen abu ne cewa tun ba yau ba, ana takun saka tsakanin tsohon kwamishinan da shugaban jam'iyyar APC na jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel