Mu na cikin matsala, Gwamnatin Buhari ta koka a kan karancin kudin shiga a Najeriya

Mu na cikin matsala, Gwamnatin Buhari ta koka a kan karancin kudin shiga a Najeriya

- Ministar tattalin arziki ta ce kudin shigan da ake samu ya na kara yin kasa

- Zainab Ahmed ta ce bukatar kudi ya na kara yawa sosai a wannan lokacin

- Ministar ta bayyana abubuwan da su ka nakasa karfin tattalin arzikin kasar

A ranar Litinin, 19 ga watan Afrilu, 2021, ministar kudi, kasafin kasa, da tsare-tsaren tattalin arziki, Zainab Ahmed, ta fito ta na kuka a kan karancin kudi.

Hajiya Zainab Ahmed ta tabbatar da cewa kudin shigan da Najeriya ta ke samu ya yi kasa. Ministar ta ce dole ne gwamnati ta zage wajen inganta harajinta.

Ministar tattalin arzikin Najeriyar ta bayyana wannan ne a lokacin da aka yi hira da ita a shirin Good Morning Nigeria a gidan talabijin na kasa watau NTA.

KU KARANTA: Yawan hatsarin tankunan da ake yi ya na damun Buhari

Da take bayani a jiya da safe, Zainab Ahmed ta ce an samu gibin Naira biliyan 50 a kudin da aka raba daga asusun hadaka na FAAC a watan jiya na Maris.

Ministar ta yi karin-haske ne a kan surutun da ake ta yi bayan gwamnan Edo, Godwin Obaseki, ya ce sai da CBN ya sake buga wasu kudi a watan da ya gabata.

Ahmed ta ce kasar ta na farfado wa ne daga matsin tattalin arzikin da ta shiga a baya, wanda sai a watannin da su ka wuce ne aka samu aka fita daga matsalar.

“Abubuwa sun yi wuya, mu na fuskantar kalubale saboda kudin shigan da mu ke samu ya yi kasa, kuma akwai bukatun kashe kudi sosai.” Inji Zainab Ahmed.

KU KARANTA: An kama wani ja'irin da ke fallasawa Boko Haram sirrin Sojoji

Mu na cikin matsala, Gwamnatin Buhari ta koka a kan karancin kudin shiga a Najeriya
Ministar tattallin arziki, Zainab Ahmed
Asali: Twitter

Ministar kudin ta ke cewa akwai bukatar a saki kudi a cikin al’umma saboda a shawo kan matsin lambar da aka shiga a sakamakon annobar cutar COVID-19.

Ministar ta ce: "A Najeriya, karyewar da farashin danyen mai ya yi, ya kawo mana cikas sosai ta wajen kudin shiga. Ba mu da isassun kudi, ga bukatu da yawa.”

Duk da halin da aka shiga, Ahmed ta ce sun rika biyan albashi da fansho, sannan an biya bashin da aka ci, amma ana kara cin wasu bashin domin ayi ayyuka.

Karamin Ministan kwadago na kasa, Festus Keyamo, ya yi karin-haske a kan wadanda aka dauka aikin SPW, ya bayyana cewa albashin wadansu ya fara shiga jiya.

Festus Keyamo SAN ya bayyana cewa ana sa ran da zarar an kammala binciken BVN a bankuna, kowane ma’aikacin da aka dauka zai rika karbar kudinsa a wata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel