Bakatsine ya yanka rago, ya shirya kayatacciyar liyafar dawowar Buhari daga London

Bakatsine ya yanka rago, ya shirya kayatacciyar liyafar dawowar Buhari daga London

- Wani dan gani kashenin shugaba Buhari ya hada liyafa don murnar dawowar da Buhari yayi daga London

- Abubakar Rabiu, wanda aka fi sani da Abu Albarka, ya yanka rago wanda aka yi shagalin dashi a wurin liyafar

- Bayan addu'o'i ga Buhari, ya kara da cewa shugaban yana daga cikin ababen alhairai da suka taba faruwa da kasar nan

Wani dan gani kashenin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya hada kayatacciyar liyafa a Katsina domin murnar dawowar shugaban kasan daga Ingila.

Abubakar Rabiu, wanda aka fi sani da Abu Albarka, ya hada liyafar a daya daga cikin fitattun gidajen cin abinci dake kallon jami'ar tarayya ta Dutsin-Ma a ranar Juma'a, 16 ga watan Afirilu.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Rabiu wanda aka sani da kaunar Buhari, ya mayar da ita al'ada, yanka rago tare da hada liyafa kowanne lokaci da Buhari ya fita kasar nan ya dawo, balle neman magani ko duba lafiyarsa. Wannan liyafar ita ce karo na takwas.

KU KARANTA: Dukkan biliyoyin da na tara sun kasa samar min da farinciki, Biloniya Otedola

Bakatsine ya yanka rago, ya shirya kayatacciyar liyafar dawowar Buhari daga London
Bakatsine ya yanka rago, ya shirya kayatacciyar liyafar dawowar Buhari daga London. Hoto daga @Lindaikeji
Asali: Twitter

KU KARANTA: Jonathan ga Aliyu: Kai babban makaryaci ne, bani da yarjejeniya da gwamnonin PDP na arewa

Bakatsine ya yanka rago, ya shirya kayatacciyar liyafar dawowar Buhari daga London
Bakatsine ya yanka rago, ya shirya kayatacciyar liyafar dawowar Buhari daga London. Hoto daga @Lindaikeji
Asali: Twitter

Liyafar ta samu halartar sauran magoya bayan shugaban kasa Buhari, wadanda suka yi buda baki tare kuma suka yi addu'ar hadin kai da cigaban Najeriya tare da tabbatar lafiyar Buhari.

"A wannan karon, kusan mutum 40 sun halarci liyafar buda bakin. Wannan ne yawan jama'a mafi karanci da suka saba zuwa irin liyafar. Ta yuwu saboda watan Ramadan ne. A liyafar karshe da muka yi, mun samu mutane kusan 300 da suka hallara," Rabiu yace.

Rabiu ya kara da cewa, shugaban kasa Buhari na daya daga cikin abubuwan alkhairi da suka taba faruwa a Najeriya balle a wannan lokaci na matsin tattalin arziki da rashin tsaro.

Yayi kira ga 'yan Najeriya da su dage wurin addu'a ga kasar nan da shugabanninta domin wanzuwar zaman lafiya, hadin kai da cigaba.

A wani labari na daban, ministan tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi mai ritaya, a ranar Lahadi, ya dira Maiduguri tare da rakiyar shugaban ma'aikatan tsaro, Janar Lucky Irabor tare da sauran hafsoshin tsaro, domin duba yanayin barnar da 'yan Boko Haram suka yi a jihar.

A yayin karbar ministan da tawagarsa a hedkwatar Operation Lafiya Dole a Maiduguri, kwamandan rundunar Manjo Janar Farouq Yahaya, ya jinjinawa yadda minstan, shugaban ma'aikatan tsaro da sauran hafsoshin tsaro ke nunawa.

Ya ce dakarun suna godiya ga ministan a kan ziyarar suke kai musu tare da tabbatar da cewa ministan tare da sauran shugabannin tsaron sun ziyarcesu bayan nada su da aka yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel