Jihohi 8 da aka kama 'yan kasuwa 400 masu daukar nauyin Boko Haram da 'yan bindiga

Jihohi 8 da aka kama 'yan kasuwa 400 masu daukar nauyin Boko Haram da 'yan bindiga

- Hukumomin DSS, NFIU, CBN tare da DIA sun bankado 'yan kasuwa 400 kuma an kama su sakamakon hannunsu a ta'addanci

- Wadanda aka kama sun hada da 'yan kasuwan canji, masu haka da siyar da zinari, da wasu 'yan kasuwa

- An kama su ne daga jihohin Kaduna, Abuja, Lagos, Zamfara, Borno, Kano, Sokoto da Adamawa

A kalla 'yan kasuwa 400 ne aka kama sakamakon zarginsu da ake yi da daukar nauyin 'yan ta'addan Boko Haram da 'yan bindiga.

Sama da shekaru 10, an kasa samun bayanai masu inganci a kan yadda mayakan ta'addanci ke samun kudi.

Kamar yadda aka gano, an kama wasu 'yan kasuwa sakamakon binciken hukumomin DIA tare da hadin guiwar DSS, NFIU da CBN.

An gano cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya amince da fara aikin binciken a 2020.

KU KARANTA: Jonathan ga Aliyu: Kai babban makaryaci ne, bani da yarjejeniya da gwamnonin PDP na arewa

Jihohi 8 da aka kama 'yan kasuwa 400 masu daukar nauyin Boko Haram da 'yan bindiga
Jihohi 8 da aka kama 'yan kasuwa 400 masu daukar nauyin Boko Haram da 'yan bindiga. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

KU KARANTA: Ta fasu: Sunayen 'yan canji a Najeriya da aka kama suna turawa 'yan Boko Haram kudi

Jaridar Daily Trust ta ruwaito yadda da farko aka samu mutum 957 da suka hada da 'yan canji, masu hakar zinari da siyarwa da sauran 'yan kasuwa da ake zargi da mugun aiki.

Wata majiya ta sanar da cewa, an kama mutum 400 a jerin jihohi kamar haka:

1. Kano

2. Borno

3. Lagos

4. Sokoto

5. Adamawa

6. Kaduna

7. Zamfara

8 Kaduna

Wadanda aka kama din suna hannun sojoji da hukumar DSS dake Abuja da sauran wurare.

"Saboda wannan bincike ne kan inda 'yan ta'adda ke samo kudi, shugaban kasa ya umarci NFIU ta jagoranci lamarin," wata majiya ta sanar.

Majiyar ta kara da cewa, bayan shugaban kasan ya amince, an hada tawaga ta manyan jami'ai wadanda aka tura karkashin DIA domin yin aikin.

"Wanda ke daukar nauyin samo kudi da zagaya shi tsakanin 'yan Boko Haram na hannunmu, shi da makusantan a kasuwan na hannunmu," yace.

A wani labari na daban, masarautar Kano ta musanta siyar da filayen Gandun Sarki wadanda yasa hukumar yaki da rashawa ta jihar kano take tuhumar Sarki Aminu Bayero da shi.

Daily Trust ta ruwaito cewa, hukumar yaki da rashawan tana bincikar masarautar akan zargin siyar da filaye har kadada 22 dake Gandun Sarki a Dorayi Karama ta karamar hukumae Gwale dake jihar Kano tare da waskar da kudin zuwa aljihunsu.

Takardun karar da wani wanda ya siya filin, Alhaji Yusuf Aliyu ya shigar, ta bukaci kotun da ta dakatar da shugaban hukumar daga hana su aikin ginin da suka fara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel