Ta fasu: Sunayen 'yan canji a Najeriya da aka kama suna turawa 'yan Boko Haram kudi

Ta fasu: Sunayen 'yan canji a Najeriya da aka kama suna turawa 'yan Boko Haram kudi

- Sunaye sun bayyana na 'yan Najeriya da aka kama da laifin turawa 'yan ta'addan Boko Haram kudi

- Da yawa daga cikinsu 'yan canji ne da masu siyar da gwal dake budaddiyar kasuwar Wapa a Kano

- Daga cikinsu akwai Baba Usaini, Abubakar Yellow (Amfani), Yusuf Ali Yusuf (Babangida), Ibrahim Shani, da sauransu

A watan da ya gabata ne Malam Garba Shehu, babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa akan yada labarai, yace gwamnatin tarayya ta kama wasu 'yan canji da ke turawa 'yan Boko Haram kudi.

Ya ce wasu 'yan Najeriya dake zama a daular larabawa (UAE) sune ke aiki da 'yan canjin wurin turawa 'yan ta'addan kudi.

"'Yan canji ne ke turawa 'yan ta'adda kudi. Tuni muka fara aiki da UAE. An samu nasarar kama wasu 'yan Najeriya dake turawa 'yan ta'addan Boko Haram kudi kuma wannan na faruwa har a cikin gida.

"Ina sanar daku, a wannan lokacin mun kammala bincike kuma 'yan Najeriya zasu sha mamaki," Shehu yace.

KU KARANTA: Boko Haram: Ministan tsaro, CDS da hafsoshin tsaro sun dira Maiduguri, Borno

Sunayen 'yan canjin da aka kama suna turawa 'yan Boko Haram kudi
Sunayen 'yan canjin da aka kama suna turawa 'yan Boko Haram kudi. Hoto daga @daily_trust
Asali: UGC

KU KARANTA: Jonathan ga Aliyu: Kai babban makaryaci ne, bani da yarjejeniya da gwamnonin PDP na arewa

Tun farko Daily Trust ta ruwaito cewa an kama mutane masu tarin yawa a binciken da aka yi na masu hada kai da Boko Haram da kuma wadanda ake zargi da tura musu kudi.

An kuma kara da gano jerin sunayen jama'an da aka kama da wannan laifin. A Kano, akwai 'yan kasuwan canji wadanda ke budaddiyar kasuwar Wapa dake karamar hukumar Fagge wadanda aka kama a watan Maris.

Fitattu daga cikin 'yan canjin da aka kama a jihar sun hada da:

Baba Usaini

Abubakar Yellow (Amfani)

Yusuf Ali Yusuf (Babangida)

Ibrahim Shani

Auwal Fagge

Muhammad Lawan Sani (mai siyar da gwal)

Hudu daga cikin 'yan canjin da aka kama suna da alaka da wasu mutum biyu da aka garkame a Dubai a shekarar da ta gabata bayan an kama su da irin wannan laifin.

Wadanda aka kama duk suna tsare ne a hannun hukumar soji ko kuma hukumar jami'an tsaron farin kaya ta Abuja da sauran wurare.

A wani labari na daban, kasa da sa'o'i hudu bayan ziyarar da minsitan tsaro, Bashir Magashi tare da hafsoshin tsaro zuwa Maiduguri, mayakan Boko Haram sun kai farmaki karamar hukumar Dikwa dake jihar Borno a ranar Lahadi.

Dikwa tana yankin tsakiyar jihar Borno ne kuma tana da nisan kilomita 85 zuwa babban birnin jihar na Maiduguri, Vanguard ta ruwaito.

Bayanan da aka samu daga majiyoyi sun tabbatar da cewa, mayakan ta'addancin dauke da makamai da motocin yaki a halin yanzu suna musayar wuta da jami'an tsaro domin su samu kutsawa garin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

iiq_pixel