Jami'o'i keda ƙarfin ikon ɗaukar sabbin ɗalibai ba wata hukuma ba, UniAbuja ta yi Martani ga JAMB

Jami'o'i keda ƙarfin ikon ɗaukar sabbin ɗalibai ba wata hukuma ba, UniAbuja ta yi Martani ga JAMB

- UniAbuja ta nesanta kanta daga zargin da hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire (JAMB) tayi mata na ɗaukar Ɗalibai ba bisa ƙa'ida ba

- Jami'ar ta bayyana haka ne ranar Litinin a wata sanarwa data fitar ta bakin mai magana da yawun jami'ar, Dr. Habib Yakoob

- Ya ce jami'ar ce keda ƙarfin ikon ɗaukar sabbin ɗalibai kamar yadda kundin tsarin jami'o'i ya tanadar ba wata hukuma daga waje ba

A ranar Litinin, jami'ar Abuja (UniAbuja) tayi martani ga hukumar JAMB kan zargin da tayi cewa jami'ar na ɗaukar ɗalibai ba bisa ƙa'ida ba.

KARANTA ANAN: Zaɓen 2023 bazai yuwu ba matuƙar ba'a magance matsalar tsaro ba, Inji tsohon Daraktan DSS

Hukumar JAMB ta zargi jami'ar ne saboda ƙin turama hukumar jerin sunayen waɗanda ta ɗauka kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

A wani jawabi da UniAbuja ɗin ta fitar, ta bakin mai magana da yawunta, Dr Habib Yakoob, ya bayyana abinda kundin tsarin mulkin jami'o'i ya tanadar game da ɗaukar sabbin ɗalibai.

Jami'o'i keda ƙarfin ikon ɗaukar sabbin ɗalibai ba wata hukuma ba, UniAbuja ta yi Martani ga JAMB
Jami'o'i keda ƙarfin ikon ɗaukar sabbin ɗalibai ba wata hukuma ba, UniAbuja ta yi Martani ga JAMB Hoto: uniabuja.edu.ng
Asali: UGC

Ya ce a sashi na 7a (ii) an bayyana cewa:

"Majalisar ƙoli ta jami'a (Senate), suke da ƙarfin iko a kan duk wani abu da ya shafi karatu kamar ƙungiyoyi da kula dasu, koyarwa da Bincike, ɗaukar sabbin ɗalibai da sauransu."

"Wannan ke tabbatar da cewa hukumar jami'a ke da ikon ɗaukar sabbin ɗalibai ba wata hukuma can daga waje ba."

KARANTA ANAN: Watan Ramadan: Gwamnatin Zamfara ta kashe 2.9 Biliyan wajen Tallafa ma talakawa a watan Ramadan

"UniAbuja bata tantama ko kaɗan cewa bata ɗauki sabbin ɗalibai ba bisa ƙa'ida ba, kuma bata da wani abu da zata boye kan matakan da take bi wajen daukar ɗalibai."

A yayin da yake bayyana jami'ar a matsayin ɗaya daga cikin jami'o'in da ake ji da su a ƙasar nan, Dr. Habib yace:

"UniAbuja kaɗai ce jami'ar da a wajen daukar sabbin ɗalibanta take duba kowanne sashi na ƙasar nan, kuma take ɗaukar ɗalibai daga kowace jiha a ƙasar nan. Ya yinda a hankali-A hankali take cigaba da zama abun yabo."

A wani labarin kuma PDP ta sake huro ma Pantami wuta, ta yi kira ga DSS ta gayyaci Ministan ya amsa tambayoyi

Jam'iyyar hamayya ta PDP ta yi kira ga hukumar tsaro ta DSS data gayyaci ministan sadarwa, Isa Pantami, yazo ya amsa tambayoyi kan zargin da ake masa.

Jam'iyyar tace ta damu matuƙa saboda ma'aikatar da Pantami ke rike da ita babbar ma'aikata ce dake ɗauke da muhimman bayanai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel