Sheikh Pantami ya bayyana wata babbar Nasarar da gwamnatin tarayya ta samu a ɓangaren Fasahar Zamani
- Ministan sadarwa da tattalin arziƙin zamani, Dr. Pantami ya bayyana babbar nasarar da shirin tsaftace ayyukan fasahar sadarwar zamani ya jawo ma gwamnatin Najeriya
- Ministan yace, yazuwa yanzun shirin na samar ma da gwamnatin Najeriya ƙarin kuɗin shiga da suka kai kimanin 22.5 biliyan
- Pantami ya faɗi haka ne a wajen bikin cika shekaru 20 da kafa hukumar dake kula da cigaban fasahar zamani (NITDA) wanda akai ma take da NITDA@20
Ministan sadarwa da tattalin arziƙin zamani, Dr. Isa Pantami yace amfani da ayyukan fasahohin zamani (IT) ya samar ma Najeriya rarar kuɗi kimanin 22.5 biliyan.
KARANTA ANAN: Shugaba Buhari ya gana da Sabon Sufetan yan sanda a karon farko bayan dawowarsa daga Landan
Ministan ya faɗi hakane a bikin cika shekara 20 da kafa hukumar samar da cigaba ta hanyar fasahar zamani (NITDA) wanda akai ma take da NITDA@20 ranar Litinin a Abuja, Dailytrust ta ruwaito.
Pantami yace duk da an ƙirƙiri NITDA a watan Afrilun shekarar 2001 a matsayin wani sashi na ma'aikatar sadarwa, ta cigaba da haɓaka har tazama tafi kowacce hukuma gudanar da ayyuka ga gwamnatin Najeriya.
Dr. Pantami yace:
"Wannan dama ce da zanyi amfani da ita in godewa dukkan waɗanda sukayi aiki a wannan hukuma tun daga sanda aka kafa ta zuwa yanzun."
"Ɗaya daga cikin nasarorin NITDA da nike alfahari dashi musamman kasancewar shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari yafi maida hankali wajen yaƙi da cin hanci, shine tsaftace ɓangaren fasahar zamani."
"Wannan aikin shine aka rasa shekaru da dama a baya amma yanzun NITDA ta sake sabunta shi."
KARANTA ANAN: PDP ta sake huro ma Pantami wuta, ta yi kira ga DSS ta gayyaci Ministan ya amsa tambayoyi
"Wannan aikin na tsaftace fasahar sadarwar zamani ya samar ma gwamnatin Najeriya ƙarin kuɗin shiga da suka kai biliyan N2bn a duk aiki ɗaya. Zuwa yanzun ya samar da kuɗi 22.5 biliyan" inji Pantami
Pantami yace hukumar NITDA ta cancanci yabo kan kiyaye ma'ajiyar bayanan Nageriya domin tabbatar da tsaro, da sirrin bayanan Najeriya.
Ya ƙara da cewa yanzun kasashe da dama na bada misali da Najeriya. "Zan iya cewa yanzun Najeriya ta zama giwar ƙasashen Africa a ɓangaren tsaro da sirrin bayanai ba wai a ɓangaren tattalin arziƙi kaɗai ba." injishi
Daga ƙarshe Pantami ya jinjina ma shugabannin NITDA bisa jagorancin su da yakai hukumar wannan babban matsayi. Ya kuma yi kira gare su, su ninka ƙoƙarinsu nan gaba.
A wani labarin kuma Gwamnatin tarayya zata ɗauki sabbin sojoji domin ƙarfafa yaƙi da Boko Haram, inji Ministan Tsaro
Ministan tsaro yace gwamnatin tarayya na shirye-shiryen ɗaukar sabbin sojoji waɗanda zasu taimaka wajen yaƙi da ta'addanci
Bashir Magashi ya bayyana haka ne yayin da ya jagoranci tawagar shugabannin tsaro suka kai ziyara ga rundunar sojojin 'Operation Lafiya Dole'
Asali: Legit.ng