Yanzu-yanzu: Bidiyon ɓarnar da gobara ta yi a ofishin INEC na Kano

Yanzu-yanzu: Bidiyon ɓarnar da gobara ta yi a ofishin INEC na Kano

- Gobara ta tashi a ofishin hukumar INEC da ke jihar Kano inda ta kone kwamfutoci da wasu kayan aiki

- Wasu da abin ya faru a gabansu sun ce lantarki ne ya saka na'urar AC ta kama da wuta

- Jami'an hukumomin kashe gobara na jiha da tarayya sun isa wurin sun kashe gobarar

Gobara ta kone wasu sassa na ofishin hukumar zabe mai zaman kanta na kasa, INEC, da ke jihar Kano, Daily Trust ta ruwaito.

Gobarar da ta fara misalin karfe 9.30 na safiyar yau a cibiyar saraffa bayanai na INEC din ta kone kwamfuta, laptop da ma dukkan ginin.

Yanzu-yanzu: Bidiyon ɓarnar da gobara ta yi a ofishin INEC na Kano
Yanzu-yanzu: Bidiyon ɓarnar da gobara ta yi a ofishin INEC na Kano. Hoto: @daily_trust
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Sheikh MaiAnnabi: Iyalan malamin Kano sun shiga fargaba yayinda wa'adin da masu garkuwa suka basu ya kusa cika

Wani shaidan gani da ido ya shaidawa majiyar Legit.ng cewa hukumomin kashe gobara na jihar Kano da na tarayya suka taru suka kashe wutar.

"Sun iso minti ashirin bayan gobarar ta tashi.

"Duk da cewa jinkirin ya saka wutar ta kone kusa dukkan ginin amma sun yi nasarar kashe wutar".

Wasu ma'aikatan hukumar wadanda abin ya faru a idonsu sun ce hauhawa da saukar karfin wutan lankarki ne ya janyo daya daga cikin na'urorin sanyaya daki da ke cibiyar ya kama da wuta.

KU KARANTA: 'Yan Boko Haram sun ji 'ba daɗi' a hannun sojoji yayin da suka yi yunƙurin ƙwace Dikwa

"A cibiyar sarafa bayannan, akwai laptop da batiri da wasu na'urori na saraffa bayanai," a cewar daya daga cikinsu.

Sun kara da cewa akwai wani akwai da ke dauke da card reader kusa da cibiyar sarrafa bayanan amma gobarar bai shafe shi ba.

Ga bidiyon yadda gobarar ta yi barna a kasa:

A wani labarin daban, direbobin motoccin haya da ke bin titin Gusau zuwa Dansadau a jihar Zamfara sun shiga yajin aikin sai baba ta gani saboda yawaitar fashi da makami da garkuwa da ke yawan faruwa a hanyar, Daily Trust ta ruwaito.

Titin ya kasance wayam babu motocci tun kwanaki hudu da suka gabata domin direbobin sun ki fitowa aiki.

Shugaban kungiyar direbobi na kasa reshen Dansadau, Isihu Ticha ya shaidawa majiyar Legit.ng cewa sun shiga yajin aikin ne domin janyo hankalin mahukunta kan halin da suke ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel