Wasu Yan bindiga sun kai hari wani ƙauye a jihar Osun, Sun harbe Mutum uku

Wasu Yan bindiga sun kai hari wani ƙauye a jihar Osun, Sun harbe Mutum uku

- Wasu yan bindiga da ba'a san ko suwaye ba sun kai hari kauyen Koka dake jihar Osun inda suka harbe mutum uku amma ba'a rasa rai ba ko ɗaya

- Mazauna garin sun tabbatar da kawo harin ranar Lahadi da misalin ƙarfe 11:30 na dare bayan wasu yan garin sun kwanta bacci

- Mai magana da yawun yan sandan jihar ta Osun, Yemisi Opalola, ya tabbatar da aukuwar lamarin amma yace basu tafi da kowa ba daga cikin mazauna kauyen

Wasu da ake zargin yan bindiga ne sun harbe mutane uku a wani hari da suka kai da tsakar dare ƙauyen Koka yankin ƙaramar hukumar Obokun jihar Osun.

KARANTA ANAN: Zaɓen 2023 bazai yuwu ba matuƙar ba'a magance matsalar tsaro ba, Inji tsohon Daraktan DSS

Wata dake zaune a ƙauyen, ta nemi a ɓoye sunanta, ta faɗa ma jaridar Punch cewa lokacin da yan bindigar suka shigo ƙauyen ta riga ta kwanta domin da tsakar dare ne misalin ƙarfe 11:30 na daren ranar Lahadi.

Tace yan bindigar sunkai su takwas, kuma da suka shigo garin sai suka raba kansu, rabinsu na shiga gidaje suna fito da mutane, sauran kuma na bin kan hanya.

Wani mazaunin garin daban kuma, Tayo Ola, yace gidan da maharan suka fara shiga bayan sun iso ƙauyen, gaba ɗaya ginin ya ɓaci da harsashin bindiga.

Wasu Yan bindiga sun kai hari wani ƙauye a jihar Osun, Sun harbe Mutum uku
Wasu Yan bindiga sun kai hari wani ƙauye a jihar Osun, Sun harbe Mutum uku Hoto: punchng.com
Asali: Twitter

KARANTA ANAN: Watan Ramadan: Gwamnatin Zamfara ta kashe 2.9 Biliyan wajen Tallafa ma talakawa a watan Ramadan

Ola ya ƙara da cewa, sun harbi mutum uku amma babu wanda suka tafi dashi, ya ce zuwan mafarauta ƙauyen yasa yan bindigar guduwa cikin daji.

Da aka tuntuɓi mai magana da yawun yan sandan jihar ta Osun, Yemisi Opalola, ya tabbatar dakai harin.

Ya ce "Wasu da ake zargin yan bindiga ne sun farmaki kauyen Kuke dake ƙaramar hukumar Obokum, sun yi ƙoƙarin sace wasu mazauna kauyen amma basu sami nasara ba."

A wani labarin kuma PDP ta sake huro ma Pantami wuta, ta yi kira ga DSS ta gayyaci Ministan ya amsa tambayoyi

Jam'iyyar hamayya ta PDP ta yi kira ga hukumar tsaro ta DSS data gayyaci ministan sadarwa, Isa Pantami, yazo ya amsa tambayoyi kan zargin da ake masa.

Jam'iyyar tace ta damu matuƙa saboda ma'aikatar da Pantami ke rike da ita babbar ma'aikata ce dake ɗauke da muhimman bayanai.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel