Hotunan wasu ƴan Nigeria da suka sake karɓar addinin musulunci a Libya

Hotunan wasu ƴan Nigeria da suka sake karɓar addinin musulunci a Libya

- Wasu maza uku sun sake karbar addinin musulunci a kasar Libya

- Mutane da dama masu amfani da dandalin sada zumunta sun tofa albarkacin bakinsu

- Wasu sun taya mazan murnar karbar addinin yayin da wasu ke ganin kamar suna da wata manufa daban

Wata kafar watsa labarai a kasar Libya ta sake ruwaito wa cewa karin wasu yan Nigeria fiye da uku sun sake karbar addinin musulunci a kasar.

A cewar rahoton da kafar watsa labaran na Libya News ta wallafa a ranar Lahadi 18 ga watan Afrilu, yan Nigeria maza uku sun ake karbar addinin musulunci a birnin Misrata, a yankin Misrata da ke nisar kilomita 187 gabashin Tripoli.

Karin wasu ƴan Nigeria sun sake karɓar addinin musulunci a Libya
Karin wasu ƴan Nigeria sun sake karɓar addinin musulunci a Libya. Hoto: Libya News Today
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Komawar wasu mata biyu Musulunci ta haifar da cece-kuce

Karbar addinin musuluncin da suka yi ya janyo hankulan yan Nigeria da mazauna Libya musulmi da kirista.

Wani Kate Marvis ya ce mutane su dena sukar wadanda suka amshi addinin na musulunci domin suna da ikon yin hakan a karkashin doka.

Ya ce, "Kowa na da ikon zabar addinin da ya ke so, idan dai ba tilasta su aka yi ba. Kada ka tilasta wa wani ra'ayin ka, wannan dama ce da kowanne dan adam ke da shi. A gani na, duk Ubangiji daya muke bautawa, ku dena cin mutuncin addini saboda halin wasu mutane, babu wanda baya kuskure, Musulmi, Kirista da Yahudawa. Na bar ku cikin aminci."

DUBA WANNAN: An yi tonon asiri tsakanin sojoji da wasu fararen hula kan taimakon ƴan Boko Haram

Ifeanyi Nathaniel ya ce, "Talauci ne ya janyo hakan."

Through D Pain ya ce, "Masha Allah, barka da zuwanku, musulunci ne addini ne na gaskiya."

Rickky Bolale ya ce, "Wannan ba wani abun damuwa bane. Duk Ubangiji daya muka bautawa. Duk da cewa larabawa ba haka suke gani ba."

A wani labarin daban, dan majalisar tarayya, Sanata Orji Uzor Kalu ya ce ya yi imanin akwai wadanda ke yunkurin yi wa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari zagon kasa.

Dan majalisar mai wakiltan Abia North a majalisar tarayya ya yi wannan furucin ne yayin wata hira da aka yi da shi a Channels TV a ranar Litinin 12 ga watan Afirilu.

Ya ce za a magance kallubalen tsaron inda aka hada kai tsakanin gwamnatin tarayya da jihohi aka yi aiki tare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel