Jihar Ondo za ta fara gwanjon shanun da ta kama da lalata gonakin 'yan jihar
- Gwamnatin jihar Ondo ta bayyana kudurinta na sanya shanun ta za ta kama na makiyaya a kasuwa
- Jihar ta ce makiyayan sun saba duk wata yarjejeniya da aka kulla tsakanin makiyaya da manoma
- Shugaban kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah ne ta sanya hannun kan yarjejeniyar a madadin makiyaya
Gwamnatin jihar Ondo ta fada a ranar Lahadi cewa daga yanzu za ta yi gwanjon shanun da aka kama da lalata gonaki bayan samun umarnin kotu, yayin da za a hukunta masu shanun da aka kama, Nigerian Tribune ta ruwaito.
Kwamandan rundunar tsaro ta jihar ta Amotekun, Cif Adetunji Adeleye ne ya bayyana hakan yayin sanya hannu kan yarjejeniyar sakin shanu sama da 250 da Amotekun suka kama a Akure, babban birnin jihar.
A cewar kwamandan, Amotekun ta kame shanu sama da 250 a cikin jihar, biyo bayan kiraye-kirayen nuna damuwa da koke-koke da manoman yankin Ipogun, Ilara, Owena Dam a karamar hukumar Ifedore ta jihar.
KU KARANTA: Lai Mohammed ya caccaki masu son a raba kasa, ya ce rikici na bullowa zasu tsere
Da yake jawabi kan matakin da jihar ta Ondo ta dauka game da yawaitar lalata gonaki, kwamandan ya ce:
“Daga yanzu za mu gurfanar da su a kotu tare da yin gwanjon shanun. Matsayin Gwamnatin Jiha da hukumar Amotekun kenan daga yanzu.
“Duk wani makiyayi da ya lalata gonaki da amfanin gona a yanzu, ba za mu bude kofar damar tattaunawa don biyan diyya ba.
“Za a kamasu, za a gurfanar da makiyayan, shanun za su zama mallakar gwamnati kuma za a yi gwanjon su saboda sassauci da muka nuna musu, ba sa ramawa dai-dai da hanyar bin yarjejeniyar da aka cimma da manoman."
Shugaban kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah, Alhaji Garba Bello, ya sanya hannu a madadin makiyaya, yayin da Mista Odeyemi Joseph da wasu mutum uku suka sanya hannu a madadin manoma.
Da yake jawabi a takaitaccen taron, Bello ya ba da tabbacin cewa makiyayan za su kiyaye yarjejeniyar, yayin da Odeyemi ya yaba wa Amotekun don amsa kira da sauri a duk lokacin da aka kira su; sannan ya ce yarjejeniyar za ta yi tasiri wajen kawo karshen lalata gonaki.
KU KARANTA: Nasara daga Allah: 'Yan sanda sun sheke 'yan bindiga 6 a jihar Neja
A wani labarin, A wani harin 'yan bindiga, akalla gidaje 50 ne suka kone tare kayan gona a wani sabon rikicin kabilanci a garin Nyuwar, na Jessu da ke jihar Gombe, The Punch ta ruwaito.
Ku tuna cewa an kashe mutane 19 tare da daruruwan gidaje da ba a san ko su waye suka lalata ba a rikicin Waja/Lunguda.
Wani shaidar gani da ido, Ily Maisanda, ya ce tuni mazauna garin suka tafi Yolde don tsare kansu, in da ‘yan bindigan suka yi amfani da wannan dama wajen kai sabon hari a Nyuwar ranar Lahadi.
Asali: Legit.ng