Dukkan biliyoyin da na tara sun kasa samar min da farinciki, Biloniya Otedola

Dukkan biliyoyin da na tara sun kasa samar min da farinciki, Biloniya Otedola

- Hamshakin mai kudi Femi Otedola, ya sanar da cewa tarin dukiyarsa bai taba samar masa da farin cikin da yake bukata ba

- A cewar Otedola, ya samu farin ciki a rayuwarsa ne bayan ya siyawa wasu yara 200 kekunan guragu kuma ya basu da hannunshi

- Otedola yace daya daga cikin yaran yace yana son tuna fuskar shi yadda idan sun hadu a aljanna zai gane shi tare da mishi godiya

Otedola ya tuna yadda yaji dadi tare da samun farin ciki bayan ya nuna kauna ga wasu yara masu nakasa wadanda ke bukatar keken guragu.

Ya bayyana irin farin cikin da ya shiga a rayuwarsa kuma yace babu abinda ya taba saka shi farinciki kamar wannan lokacin a duniya.

Otedola yace: "Na taba shiga wasu matakai hudu na farinciki a rayuwa kuma daga karshe na gane ma'anar farinciki na hakika. Mataki na farko shine tara dukiya da suna. Amma a wannan matakin, ban samu farin cikin da nake bukata ba.

KU KARANTA: Zamfara: 'Yan sanda sun kama likita, jami'an tsaro 2 da wasu mutum 5 da hannu a ta'addanci

Dukkan biliyoyin da na tara sun kasa samar min da farinciki, Biloniya Otedola
Dukkan biliyoyin da na tara sun kasa samar min da farinciki, Biloniya Otedola. Hoto daga lailasnews.com
Asali: UGC

KU KARANTA: NDLEA ta damke 'yan kasar Chadi da Nijar dake samarwa 'yan ta'adda miyagun kwayoyi

"A haka na tarar da mataki na biyu, wanda na tara kadarori da kaya. Amma kuma sai na gane cewa wannan ne takaitaccen lokaci ne kuma kyalkyalin su baya dadewa.

"A mataki na uku, na fara samun manyan ayyuka. A lokacin ne nake samar da man dizal kashi 95 na Najeriya da Afrika. Amma ko a nan, ban samu farin cikin da nake bukata ba.

"A mataki na hudu ne wani abokina ya bukaci in siyawa wasu yara keken guragu. Kusan yara 200. Babu jimawa na siyawa yaran. Amma sai abokin yace mu je tare mu mika musu. Na shirya muka je tare na basu da kaina."

Wani yaro yace min: "Ina so in tuna fuskarka yadda idan mun hadu a aljanna, zan iya ganeka kuma in kara maka godiya."

A wani labari na daban, shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi bayanin dalilin da yasa ya zabi Alkali Baba a matsayin sabon mukaddashin sifeta janar na 'yan sandan Najeriya.

Bayan sanarwar da aka yi, mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya kawata IGP a ranar 7 ga watan Afirilu yayin da Buhari yake kasar Landan domin duba lafiyarsa.

Wannan sanarwan ta nadin sabon IGP ya janyo cece-kuce inda wasu ke ganin bai dace ba a kundin tsarin mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: