Boko Haram: Ministan tsaro, CDS da hafsoshin tsaro sun dira Maiduguri, Borno
- Manjo Janar Bashir Magashi mai ritaya tare da sauran hafsoshin tsaro sun isa Maiduguri dake jihar Borno
- Ministan tsaro tare da sauran hafsoshin tsaron kasar sun isa ne domin yanayin barnar da Boko Haram suka tafka
- Dakarun sojin kasar ta bakin kwamandan OPD, ya jinjinawa hafsoshin tsaron da ministan a kan ziyarar da suka kai
Ministan tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi mai ritaya, a ranar Lahadi, ya dira Maiduguri tare da rakiyar shugaban ma'aikatan tsaro, Janar Lucky Irabor tare da sauran hafsoshin tsaro, domin duba yanayin barnar da 'yan Boko Haram suka yi a jihar.
A yayin karbar ministan da tawagarsa a hedkwatar Operation Lafiya Dole a Maiduguri, kwamandan rundunar Manjo Janar Farouq Yahaya, ya jinjinawa yadda minstan, shugaban ma'aikatan tsaro da sauran hafsoshin tsaro ke nunawa.
Ya ce dakarun suna godiya ga ministan a kan ziyarar suke kai musu tare da tabbatar da cewa ministan tare da sauran shugabannin tsaron sun ziyarcesu bayan nada su da aka yi.
KU KARANTA: NDLEA ta damke 'yan kasar Chadi da Nijar dake samarwa 'yan ta'adda miyagun kwayoyi
KU KARANTA: Zamfara: 'Yan sanda sun kama likita, jami'an tsaro 2 da wasu mutum 5 da hannu a ta'addanci
Kamar yadda Vanguard ta wallafa, Yahaya yayi bayanin cewa bayan ziyarar da shugabannin tsaron suka kai karkashin shugabancin shugaban ma'aikatan tsaro, sauran shugabannin tsaro sun kai ziyara daya bayan daya.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa ministan da tawagarsa sun shiga taron sirri tare da kwamnadojin hedkwatoci.
A wani labari na daban, Samuel Ortom, gwamnan jihar Benue, ya ce bai sake iya runtsa bacci ba tun bayan da aka kashe sojoji 11 a jiharsa. An kashe sojojin a kauyen Bonta dake karamar hukumar Konshisha a Benue.
Gwamnan a ranar Laraba ya yi wa shugaban kasan ta'aziyya tare da rundunar sojin a kan lamarin da ya faru, The Cable ta ruwaito.
Ya yi wannan jawabin ne yayin da Bashir Magashi, ministan tsaro da kuma hafsoshin tsaro suka kai masa ziyara a Makurdi.
"Ban yi bacci ba tun bayan kashe sojoji da aka yi," gwamnan yace.
Ortom ya mika godiya ga jami'an tsaro a kan goyon bayansu da gudumawarsu, ballantana sojoji dake tabbatar da zaman lafiya a jihar.
Asali: Legit.ng