Ka fito ka faɗa mana gaskiyar rashin lafiyar dake damunka, Bishop Wale Ga Buhari

Ka fito ka faɗa mana gaskiyar rashin lafiyar dake damunka, Bishop Wale Ga Buhari

- Shugaban ƙungiyar mabiya addinin kirista, Bishop Wale Oke, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da Shugaba Buhari da su daina wani boye-boye game da rashin lafiyar da shugaban ke fama da ita

- Oke ya ce ya kamata kowanne ɗan Najeriya ya san halin da shugaban ƙasa yake ciki don yasan tayadda zai masa addu'a kai tsaye

- Ya ce akwai babbar barazana ace shugaban mu yana zuwa hannun wasu duba lafiyarsa bayan ya tsallake mu.

Bishop Wale Oke, shugaban wata ƙungiyar mabiya addinin kirista (PFN), ya roƙi gwamnatin Najeriya da ta daina boye gaskiya game da rashin lafiyar da Shugaban ƙasa Buhari ke fama da ita.

KARANTA ANAN: Yan sanda sun kama wata mata da zargin ta kashe ɗan kishiyarta da guba

Oke ya bayyana cewa shugaban ƙasa ba mutum ne mai zaman kansa ba kuma yakamata ya rinƙa bayyana abin da ke damushi domin kiristoci susan yadda zasu mishi addu'a.

Biship Oke wanda ya yi wannan jawabi a wani taro a Lagos, ya ce:

"Muna ma shugaban mu addu'a ya samu lafiya, ya fita ƙasar nan na tsawon makonni biyu saboda dalilin rashin lafiya. Sai dai abu biyu na damun mu akan fita neman lafiƴar da shugaban ƙasar mu ke yi."

"Da farko muna damuwa sabida ba'a bayyana mana asalin gaskiyar abunda ke damunsa ba, muna kira ga gwamnatin tarayya da kuma fadar shugaban ƙasa, su fito su bayyana mana abunda ke damun shugaban ƙasar mu."

Kadaina wani Ɓoye-Ɓoye, Ka fito ka faɗa mana gaskiyar rashin lafiyar dake damunka, Bishop Wale Ga Buhari
Kadaina wani Ɓoye-Ɓoye, Ka fito ka faɗa mana gaskiyar rashin lafiyar dake damunka, Bishop Wale Ga Buhari Hoto: independent.ng
Asali: Twitter

"Yanzun shi ba mutum ne mai zaman kanshi ba, shugaban ƙasar mu ne, yakamata musan meke damunshi saboda mu masa addu'a kai tsaye. Ku daina ɓoye mana rashin lafiyar shugaban ƙasa, ku fito ku bayyana ma yan ƙasa komai, daga nan musan me yakamata mu yi."

KARANTA ANAN: Kotu ta yanke ma fitacciyar jarumar shirya fina-finai hukuncin watanni uku a gidan yari saboda hoton tsiraici

Hakanan kuma Oke ya yi mamakin dalilin da yasa shugaban ƙasa Buhari ya zaɓi ya fita ƙasar waje neman lafiya kamar yadda PM News ta ruwaito.

Ya ce: "Abu na biyu shine, muna damuwa a duk lokacin da shugaban mu yake buƙatar duba lafiyar sa, sai ya fita ƙasar waje. A wajen mu wannan babbar barazana ce ga tsaronsa. Abun tambayar shine; shin yafi tsaro ne ya faɗa hannun yan ƙasar waje da ace yana hannun mu?"

"Mu ɗauka mutanen nan suna da burin cutar da ƙasar mu, idan suka yima shugaban mu wani abu ya ya zamu yi?"

Bishop Oke ya ƙara roƙon gwamnatin tarayya da ta ƙasa zage damtse kan babban ƙalubalen dake gabanta na tsare lafiyar yan Najeriya baki ɗaya.

A cewarsa, kowanne ɗan Najeriya ya damu matuƙa a kan matsalolin tsaron da suka addabi ƙasar nan.

A wani labarin kuma Ministan Wutar Lantarki ya nemi gafarar yan Najeriya bisa saka su a duhu

Ministan wutar lantarki, Sale Mamman ya roƙi gafarar yan Najeriya sabida matsalar rashin wutar lantarki da yan Najeriya suka fuskanta kwanan nan.

Ministan ya dangata hakan da lalacewar tashoshin samar da wutar da kuma rabata, amma ya tabbatar da ma'aikatarsa na aiki tuƙuru wajen warware matsalar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel