Jerin jihohin da ke da mafi yawa da karancin kudaden shiga a 2020

Jerin jihohin da ke da mafi yawa da karancin kudaden shiga a 2020

A ranar Juma’a, 16 ga Afrilu, Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta buga Harajin Cikin Gida (IGR) na jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya (FCT) na zango na 4 na shekarar 2020 da kuma na shekara guda.

Rahoton ya nuna cewa jihohi 36 da FCT sun hada IGR na triliyan N1.31 a 2020.

KU KARANTA KUMA: Ni ba dan ta'adda bane; direba na da sakatariya ta Kiristoci ne, Pantami

Legit.ng ta lura cewa adadin IGR 2020 yayi kasa da na 2019 wanda yakai triliyan N1.33. Idan aka hada IGR ɗin an samu ragi na -1.93% na shekara-shekara(2019/2020).

Jerin jihohin da ke da mafi yawa da karancin kudaden shiga a 2020
Jerin jihohin da ke da mafi yawa da karancin kudaden shiga a 2020 Hoto: @jidesanwoolu, @GovWike, @MuhdMusaBello, @IAOkowa, @GovKaduna
Asali: Twitter

A cewar rahoton, har yanzu jihar ta Legas ta fi sauran karfi da IGR na N418.99 biliyan. Jiha guda daya tak da ke kusa da Legas ita ce Ribas wacce ta samu biliyan N117.19.

Wannan zaure yana nuna manyan jihohin 10 da ke da IGR mafi tsoka da jihohi biyar da ke da mafi ƙarancin IGR.

Jihohi 10 da ke da mafi girman IGR

1. Lagos - N418.99 biliyan

2. Ribas - N117.19 biliyan

3. FCT - N92.05 biliyan

4. Delta - N59.73 biliyan

5. Kaduna - N50.76 biliyan

6. Ogun - N50.74 biliyan

7. Oyo - N38.04 biliyan

8. Kano - N31.81 biliyan

9. Akwa Ibom - N30.69 biliyan

10. Anambra - N28.00 biliyan

Jihohi biyar da ke da mafi kankantar IGR

1. Jigawa - N8.66 biliyan

2. Gombe - N8.53 biliyan

3. Adamawa - N8.32 biliyan

4. Taraba - N8.11 biliyan

5. Yobe - N7.77 biliyan

A gefe guda, hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) a ranar Alhamis, 11 ga watan Fabrairu, ta fitar da rahoton yadda aka kasafta kudin Disamba 2020 na kudin wata-wata da ake rarrabbawa daga asusun gwamnatin tarayya (FAAC).

A cewar NBS, FAAC ta raba kudi naira biliyan 601.11 a tsakanin bangarorin uku na gwamnati, wato gwamnatin tarayya, jihohi da kananan hukumomi, a watan Disambar 2020 daga kudaden shigar da aka samu a watan Nuwamba 2020.

Legit.ng ta kawo yawan kudin da gwamnatocin tarayya, jihohi da kananan hukumomi suka samu da kuma sauran muhimman bayanai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel