Babu jaruman shugabanni a Nigeria da za su faɗawa Buhari gaskiya, Ortom

Babu jaruman shugabanni a Nigeria da za su faɗawa Buhari gaskiya, Ortom

- Gwamnan Benue, Samuel Ortom ya ce babu jaruman shugabanni da za su iya fadawa gwamnatin tarayya gaskiya a Nigeria

- Ortom ya yi wannan furucin ne a jawabinsa wurin taron da kungiyar yan jarida, NUJ, ta shirya a babban birnin tarayya Abuja

- Gwamnan ya ce wasu daga cikin manyan yan Nigeria sun fada masa suna goyon bayan dokarsa na hana kiwo a Benue amma ba su iya fitowa fili su fada

Samuel Ortom, gwamnan jihar Benue ya ce Nigeria ba ta da jaruman shugabanni da za su iya fadawa gwamnatin tarayya gaskiya, The Cable ta ruwaito.

A jawabin da ya yi wurin taron da NUJ ta shirya a Abuja, Ortom ya ce kasar ba ta da shugabanci nagari da zai ceto ta daga matsalolin da ta ke fama da su.

Nigeria ba ta da jaruman shugabanni da za su faɗawa Buhari gaskiya, Ortom
Nigeria ba ta da jaruman shugabanni da za su faɗawa Buhari gaskiya, Ortom. @thecableng
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Yadda mutanen gari suka kashe 'yan bindiga 30 a Katsina

Ya ce yadda ake garkuwa da mutane da kai wa mutane hare-hare a kasar abu ne mai ban tsaro.

"Na fahimci cewa Najeriya nada matsalar shugabanci na nagari. Akwai alamar ba mu da jaruman shugabanni da za su fahimci abin da ke da kyau su fadawa kasar," in ji Ortom.

"Muna da matsorata da ke yawo suna kiran kansu jagororin kasa da yankuna amma ba su iya magana su fadawa gwamnatin tarayya gaskiya ko su bata shawara yadda ya dace.

"Shugabanni da yawa sun fada min suna goyon bayan dokar da muka yi na hana kiwo domin yin adalci ba ma a Benue kadai ba har da kasa baki daya. Amma ba za su iya fitowa filli su fada ba."

KU KARANTA: Komawar wasu mata biyu Musulunci ta haifar da cece-kuce

Gwamnan ya kara da cewa akwai zargin da ake yi na cewa wasu yan siyasa marasa hakuri ne suka dako hayar mayaka daga kasashen waje domin su taimake su cin zabe.

A wani labarin daban, direbobin motoccin haya da ke bin titin Gusau zuwa Dansadau a jihar Zamfara sun shiga yajin aikin sai baba ta gani saboda yawaitar fashi da makami da garkuwa da ke yawan faruwa a hanyar, Daily Trust ta ruwaito.

Titin ya kasance wayam babu motocci tun kwanaki hudu da suka gabata domin direbobin sun ki fitowa aiki.

Shugaban kungiyar direbobi na kasa reshen Dansadau, Isihu Ticha ya shaidawa majiyar Legit.ng cewa sun shiga yajin aikin ne domin janyo hankalin mahukunta kan halin da suke ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel