Malaman addinin Kirista sun yi bude bakin Ramadana da yan uwa Musulmi

Malaman addinin Kirista sun yi bude bakin Ramadana da yan uwa Musulmi

- Malaman addinin Kirista sun taya yan uwa Musulmi yin bude baki na azumin Ramadana a Kaduna

- Jagoran tawagar Kiristocin, Fasto Yohanna Buru, ya ce duk shekara sukan hadu da manyan malaman Musulunci don yin bude baki a kokarinsu na wanzar da zaman lafiya da aminci

- Buru ya kuma jaddada cewa yin hakan ba yana nufin ya bar addininsa bane, inda ya karfafawa yan uwansa Kiristoci yin abunda zai kawo dankon soyayya tsakaninsu da Musulmai

Wasu malaman addinin kirista a kaduna sun bi sahun takwarorinsu na musulmai wajen buda baki cikin azumin watan ramadan domin karfafa juriya ta addini, zaman lafiya, soyayya, yafiya da kyakkyawar fahimta a tsakanin su.

Da yake magana a lokacin buda baki, Jagoran tawagar, shuaban cocin Christ Evangelical and Life Intervention Ministry, Sabon Tasha, Kaduna, Fasto Yohanna Buru, ya ce a shekaru 11 da suka gabata, yana zaman bude baki da manyan malaman addinin Musulunci na Najeriya.

Ya ce yana hakan ne don inganta haƙuri da addini a fadin jihohi 36 na Najeriya, Jamhuriyar Nijar da sauran ƙasashe da ke maƙwabtaka, jaridar PM News ta ruwaito.

Malaman addinin Kirista sun yi bude bakin Ramadana da yan uwa Musulmi
Malaman addinin Kirista sun yi bude bakin Ramadana da yan uwa Musulmi Hoto: PM News
Asali: UGC

KU KARANTA KUMA: APC ta yi babban rashi yayinda manyan jiga-jiganta 2 suka koma PDP tare da Magoya baya 1,000

Buru ya ce an yi ziyarar ne da nufin karfafa alakar Kirista da Musulmai a jihar, don kara karfafa zaman tare da aminci, hakuri da addini, yafiya a tsakanin ‘yan Nijeriya, tare da yada sakon Zaman lafiya da hadin kai don kauce wa dukkan nau’ikan rikicin addinai, siyasa da bambancin yanki.

Fasto Buru, ya samu rakiyar Reverend Paul da John Moses da sauran mambobin cocin zuwa gidan Malam Rilwanu Abdullahi da ke Kakuri-Makera, Kudancin Kaduna.

Sun yi nuni da cewa buda baki yana basu damar inganta ayyukan addinai da yada sakonnin zaman lafiya da kyakkyawar fahimta, ta yadda za su zauna cikin lumana da jituwa da dukkan bil'adama.

Buru ya ce “duk shekara yakan ziyarci manyan shugabannin addinin Musulunci da malamai na Najeriya da suka hada da Sarkin Musulmi, Dr. Sa'ad Abubakar, Shiekh Dahiru Bauchi, Shiekh Ibrahim El-Zakzaky, Shiekh Salihu Mai-Barota, Shiekh Ibrahim Yaya, Alaramma Abdulrahman Mohammed Bichi yayin Azumin Ramadan.

“Mun zo tare da malamanmu ne don mu kulla kyakkyawar alaka da Musulmi da kuma malamanmu na addini.

"Dole ne mu kaunaci makwabtanmu Musulmai, shi ya sa muke nan tare da su don nuna murnar shigowar watan Ramadan tare da jan hankalinsu da su sadaukar da rayukansu ga bautar Allah," in ji shi.

Ya ce Najeriya na fuskantar mawuyacin lokaci a yayin da ake fama da annobar COVID-19, don haka akwai bukatar hada hannu da kowane mai ruwa da tsaki tare da yin addu'ar zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.

Fasto Buru ya kara bayyana cewa shugabannin addinin kirista duk shekara suna zuwa gidan yari na Najeriya don bayar da belin wasu ‘yan uwa musulmai domin su samu damar yin azumin su a gida tare da abokai da dangi kamar kowane mutum, sannan kuma su halarci Tafsiri .

Buru ya jaddada cewa shiga cikin musulmai wajen yin buda baki na Ramadan ba zai canza addininsa ba, kuma ya karfafa wa sauran shugabannin kiristoci su nemi hanyoyin karfafa ayyukan addinai.

Da yake mayar da martani, Malam Rilwanu Abdullahi ya nuna jin dadinsa game da ziyarar tare da gode wa dukkan malaman addinin Kirista da suka ba shi hadin kai wajen yin buda bakin Ramalana da nufin bunkasa zaman lafiya da hadin kai a tsakanin ’yan Najeriya.

KU KARANTA KUMA: 2023: Ribas ce zata tantance wanda zai gaji Buhari, Wike ya bayyana

Abdullahi ya ce zaman lafiya shi ne abin da muke bukata a Najeriya da ma duk duniya, yana mai jaddada cewa Allah ne kadai zai iya saka wa Fasto Yohanna da kyakkyawar niyyar bunkasa zaman lafiya a kasar.

A wani labarin, wasu 'yan bindiga da har yanzu ba a gano ko su waye ba a yammacin ranar Alhamis sun tsinkayi fadar Obadu na Ilemeso dake Ekiti a jihar Ekiti.

Sun sace basaraken mai suna Oba David Oyewumi kuma sun yi awon gaba dashi zuwa inda har yanzu ba a gano ba, Leadership ta ruwaito.

Ilemeso na daya daga cikin yankunan karamar hukumar Oye dake jihar wacce ake yawaita satar jama'a domin karbar kudin fansa a watanni kadan din nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel