Jerin jihohi 5 da suka fi aiwatarwa al'ummarsu manyan ayyuka na kasafin kudi, Kaduna ce ta farko
Ayyukan da gwamnatocin jihohi da tarayya ke yiwa al'umma ya kasu kashi biyu; manya da sabbin ayyuka da kuma ayyukan yau da kullum.
A saukake, manyan ayyuka sune ayyukan da suka hada da hanyoyi, asibitoci, makarantu, dss.
Ayyukan yau da kullum kuwa sune albashi, fansho, alawus da da sauran su.
Tsakanin wadannan ayyuka, manyan ayyuka sun fi muhimmanci wajen cigaban tattalin arzikin jihar, a cewar BudgIT.
BudgIT tace: "Iya adadin kudin da gwamnati ta zuba cikin manyan ayyuka, iya irin ingantuwar tattalin arzikinta."
A sabon rahoton da BudgIT ta fitar, ta hararo jihohin da suka fi yiwa al'ummarsu manyan ayyukan da suka tsara a kasafin kudin 2019.
DUBA NAN: Wadanda suka yi garkuwa da dalibai a Kaduna sun fara kiran iyayen domin kudin fansa
KU KARANTA: Ba ni na raba shinkafa a Kano ba amma ina godiya ga wadanda sukayi, Tinubu
Ga jerin jihohi 5 mafi aiwatar da kasafin kudin 2019:
1. Jihar Kaduna
Kudin manyan ayyukan da aka kasafta : N152.3bn
Kudin da aka kashe kan manyan ayyuka: N148.3bn
Alkalamin aiwatarsa: 97.53%
2. Jihar Yobe
Kudin manyan ayyukan da aka kasafta : N39.5bn
Kudin da aka kashe kan manyan ayyuka: N30.1bn
Alkalamin aiwatarsa: 76.21%
3. Jihar Rivers
Kudin manyan ayyukan da aka kasafta : N301.5bn
Kudin da aka kashe kan manyan ayyuka: N224.1bn
Alkalamin aiwatarsa: 69.81%
4. Jihar Lagos
Kudin manyan ayyukan da aka kasafta : 345.3bn
Kudin da aka kashe kan manyan ayyuka: 241.1bn
Alkalamin aiwatarsa: 69.81%
5. Jihar Jigawa
Kudin manyan ayyukan da aka kasafta: 90.1bn
Kudin da aka kashe kan manyan ayyuka: 61.9bn
Alkalamin aiwatarsa: 67.99%
A bangare guda, Nyesom Wike, gwamnan jihar Ribas, ya ce duk wanda ke neman zama shugaban kasa a 2023 zai bukaci samun kuri'u a Ribas sannan ya hada kai da Kano ko Legas don samun nasara.
Jaridar The Nation ta rahoto cewa ya ce irin wannan gagarumar matsayar ce ta tabbatar da mahimmancin Ribas a cikin tsarin siyasar kasar nan, yana mai cewa babu wanda za a bari ya bata shi.
Asali: Legit.ng