Zamfara: 'Yan sanda sun kama likita, jami'an tsaro 2 da wasu mutum 5 da hannu a ta'addanci

Zamfara: 'Yan sanda sun kama likita, jami'an tsaro 2 da wasu mutum 5 da hannu a ta'addanci

- 'Yan sandan jihar Zamfara sun damke wani likita da wasu mutum 7 a kan zargin hannunsu a taimakon 'yan bindiga

- Daga cikin sauran mutum 7 da aka kama, akwai jami'an tsaro biyu wadanda suka amsa cewa suna tallafawa 'yan bindigan

- An kama su ne tafe da kayan sojoji, bindigogi da harsasai, a kan hanyarsu ta kaiwa wasu 'yan bindiga a Sokoto

Rundunar 'yan sandan jihar Zamfara ta damke wani likita tare da wasu mutum 7 a kan zarginsu da ake yi da taimakawa 'yan bindiga a fadin jihar.

Kwamishinan yada labarai na jihar, Ibrahim Dosara, ya bayyana wannan a jawabin da yayi wa manema labarai a Gusau a ranar Alhamis inda yace an kama likitan a kauyen Kamarawa dake karamar hukumar Isa ta jihar Sokoto.

Kwamishinan yace jami'an rundunar Operation Puff Adder ne suka kama likitan a zarginsa da suke masa na samar da kayan sojoji ga 'yan bindigan.

KU KARANTA: Katsina: An yankewa gagarumin dilan miyagun kwayoyi hukuncin shekaru 15 a gidan yari

Zamfara: 'Yan sanda sun kama likita da wasu mutum 7 masu taimakon 'yan bindiga
Zamfara: 'Yan sanda sun kama likita da wasu mutum 7 masu taimakon 'yan bindiga. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

KU KARANTA: Angon da ya bace ranar bikinsa ya bayyana, yace gidan abokinsa ya je huce gajiya

Bayan binciken farko, an samu takalman sojoji 10, da wasu jerin kayayyaki daga hannun shi.

Dosara ya kara da bayanin cewa biyu daga cikin wadanda ake zargin bakwai akwai jami'an tsaro, an tuhumesu kuma da bakinsu sun amsa yadda suke da hannu wurin zagon kasa ga ayyukan soji dake jihar.

Ya kara da cewa kamar yadda wadanda ake zargin suka sanar, suna samar da kayan sojoji, makamai, bayanan sirri na sojin da sauran abubuwa ga 'yan bindigan.

Wani wanda aka kama da ake zargin yana hada kai da 'yan bindigan da kuma samar musu da makamai ya amsa laifinsa.

Hakazalika, Dosara yace wani wanda ake zargin daga Sokoto an kama shi yana samar da kayan sojoji ga wasu 'yan bindiga.

Ya kara da cewa, "An samu kayan sojoji tara, sai safar hannu saiti biyar na sojin sama, ATM biyu, katin shaida na sojin kasa da wayar hannu kirar Samsung."

A wani labari na daban, wata mai rajin kare hakkin dan Adam mai suna Oluwatosin Adeniji, ta zargi Omoyele Sowore da neman tallafi da sunanta kuma ya samu ya adana.

A ranar Talata, 14 ga watan Afirilu ne ta je shafinta na Twitter inda tayi yayata ga Sowore akan yadda ya nemi tallafi da sunanta ba tare da ta sani ba.

Wani sashin wallafarta yace: "Sowore, abun takaici ne yadda kayi amfani da sunana tare da wahalar da na sha. Na je gidan yari a watan Nuwamban shekarar da ta gabata a kan EndSARS amma ka nemi tallafi da sunana ba tare da ka sanar dani ba."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng