Angon da ya bace ranar bikinsa ya bayyana, yace gidan abokinsa ya je huce gajiya

Angon da ya bace ranar bikinsa ya bayyana, yace gidan abokinsa ya je huce gajiya

- Ranar Asabar, 10 ga watan Afirilu ne ya kamata ya zama babbar rana ga Christabella da Patrick

- Amma kuma ta kasance ta tashin hankali bayan Patrick yayi batan dabo a yammacin jajiberin bikinsu

- Bayan wasu kwanaki, ya bayyana kuma yace gajiya ce tasa ya tafi gidan abokinsa inda ya kwashe kwanakin

Wani ango yayi batan dabo a ranar bikinsa kuma kamar yadda yace, yayi hakan ne domin ya samu ya huta a gidan abokinsa saboda gajiyar da yayi.

Kamar yadda Daily Monitor ta ruwaito, Dr Patrick Mbusa Kabagame da Christabella Banturaki sun shirya auren a All Saints Cathedral Nakasero dake birnin Kampala a ranar Asabar, 10 ga watan Afirilu. An shirya liyafa a otal na Silver Springs dake Kampala.

Amma kuna a yammacin ranar mai cike da tarihi, Dr Kabagame yayi batan dabo kuma ya kashe wayarsa. Wannan ya tsorata jama'a kuma 'yan uwa, abokan arziki da sirikai sun fada tashin hankali.

Amaryarsa tare da kawunta sun garzaya ofishin 'yan sanda na Kasangati dake yankin Wakiso inda suka kai korafi kan batan angon.

Babu bata lokaci jami'ai, 'yan uwa da abokan arziki suka fara neman angon. Tuni aka cika kafafen sada zumuntar zamani da hotuna tare da sanarwar batan Dr Kabagambe.

KU KARANTA: Sojan ruwa ya sokawa sojan sama wuka bayan ya kama shi turmi da tabarya da matarsa

Angon da ya bace ranar bikinsa ya bayyana, yace gidan aboki ya je hutawa
Angon da ya bace ranar bikinsa ya bayyana, yace gidan aboki ya je hutawa. Hoto daga Daily Monitor
Asali: UGC

KU KARANTA: Ku tuhumi magabatana a kan kudin makamai ba ni ba, COAS ga majalisar tarayya

Amma kuma bayan kwanaki biyu, angon ya bayyana inda ya mika kansa ofishin 'yan sanda na Wandegeya dake Kampala kuma yace ba bacewa yayi ba.

"Yace gajiya ce ta dame shi. Bashi da dalilin da zai hana shi auren Banturaki. Mun sake shi yayin da 'yan sanda suka cigaba da bincike," Luke Owoyesigyire, dan sanda a birnin Kampala ya sanar da hakan a ranar Litinin, 12 ga watan Afirilu.

A wani labari na daban, gwamnatin jihar Bauchi ta ce zata gudanar da kidayar mata masu zaman kansu da suke fadin jihar don sanin asalin yawansu a jihar, Premium Times ta wallafa.

Aminu Balarabe-Isah, kwamishinan Hisbah da Shari'a ya bayyana hakan a Bauchi ranar Litinin yayin tattaunawa da mata masu zaman kansu na jihar.

A cewarsa, samun asalin yawansu don sanin yadda zasu bullo wa lamarin zai taimaka wurin kawo karshen wannan mummunar sana'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng