Mai rajin kare hakkin dan Adam ta zargi Sowore da karbar tallafi da sunanta babu izininta

Mai rajin kare hakkin dan Adam ta zargi Sowore da karbar tallafi da sunanta babu izininta

- Wani rikici ya rincabe a kafar sada zumuntar zamani ta Twitter a Najeriya

- Mai rajin kare hakkin dan Adam, Omoyele Sowore ake zargi da muguwar damfara

- Daya daga cikin manyan mukarrabansa ta zargesa da amfani da sunanta wurin samun tallafi babu izininta

Wata mai rajin kare hakkin dan Adam mai suna Oluwatosin Adeniji, ta zargi Omoyele Sowore da neman tallafi da sunanta kuma ya samu ya adana.

A ranar Talata, 14 ga watan Afirilu ne ta je shafinta na Twitter inda tayi yayata ga Sowore akan yadda ya nemi tallafi da sunanta ba tare da ta sani ba.

Wani sashin wallafarta yace: "Sowore, abun takaici ne yadda kayi amfani da sunana tare da wahalar da na sha. Na je gidan yari a watan Nuwamban shekarar da ta gabata a kan EndSARS amma ka nemi tallafi da sunana ba tare da ka sanar dani ba."

KU KARANTA: Gwamnatin Bauchi za ta yi kidayar mata masu zaman kansu mazauna jihar

Mai rajin kare hakkin dan Adam ta zargi Sowore da karbar tallafi da sunanta babu izininta
Mai rajin kare hakkin dan Adam ta zargi Sowore da karbar tallafi da sunanta babu izininta. Hoto daga @YeleSowore
Asali: Twitter

KU KARANTA: Sojan ruwa ya sokawa sojan sama wuka bayan ya kama shi turmi da tabarya da matarsa

Lauyan da aka zarga da hannu a ciki tuni ya bada labarinsa ta shafinsa na Twitter. Wani sashi na wallafar yace: "Ban taba neman tallafi da sunan Adeniji ba. Ban taba kuma samun kowanne irin tallafi ba saboda rajin kare hakkin dan Adam da nake yi.

"Sowore da Tosin sun san haka. Amma abun takaici ne yadda daya daga cikinsu ke rufa-rufa."

Sowore da kan shi yayi bayani a kan lamarin a shafinsa na Twitter. Wani sashin wallafar yace: "Tun farko Adeniji ta zo min da zancen cewa an nemi tallafi da sunanta kuma tuni na tabbatar mata da cewa hakan bata faru ba.

"Har ila yau nace zan biya ta ko nawa ne in har an karba tallafin ba tare da saninta ba."

A wani labari na daban, tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, ya shiga hannun hukumar yaki da rashawa da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, jaridar Premium Times ta tabbatar.

Jami'an hukumar EFCC sun kama Okorocha wurin karfe 4 na yammacin Talata a ofishinsa dake Abuja, majiya ta tabbatar.

Majiyar da ta tabbatar, ta ce hukumar ta dinga tura gayyata ga tsohon gwamnan zuwa ofishinta dake Abuja saboda harkallar wasu kudade amma ya ki zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng