Yanzu-Yanzu: EFCC ta sako tsohon gwamna Okorocha bayan kwanaki biyu a tsare

Yanzu-Yanzu: EFCC ta sako tsohon gwamna Okorocha bayan kwanaki biyu a tsare

- Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta sako tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha

- Hadiminsa tsohon gwamnan ya tabbatar da cewa Okorocha ya koma gidansa da ke Maitama a Abuja

- EFCC ta kama Okorocha ne a ranar Talata a ofishinsa ta kuma tafi ta tsare shi na kwanaki biyu kan zargin almundahana lokacin yana gwamna

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati, EFCC, ta sako tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha bayan ya yi kwanaki biyu a hannunta yana amsa tambayoyi.

Hadimin Okorocha, wanda ya yi magana da Daily Trust a wayar tarho ya ce an sako tsohon gwamnan misalin karfe 5.45 na yamma kuma a halin yanzu yana gidansa da ke Maitama a Abuja.

DUBA WANNAN: Gwamnonin Arewa sun yi wa Rundunar Sojoji ta'aziyyar kisar dakarunta 12 a Konshisha

Yanzu-Yanzu: EFCC ta sako Okorocha bayan tsare shi na kwanaki biyu
Yanzu-Yanzu: EFCC ta sako Okorocha bayan tsare shi na kwanaki biyu. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Mutum 10 sun mutu, wasu 500 na asibiti bayan shan gurbataccen sinadari a Kano

Da aka tuntube shi, mai magana da yawun hukumar na yaki da rashawa, Wilson Uwujaren ya ce a bashi lokaci kafin ya yi tsokaci kan lamarin.

A ranar Talata ne jami'an EFCC suka kama dan majalisar a ofishinsa da ke Unity House Garki Abuja misalin karfe 4 na yamma.

Ana zargin Okorocha, wanda ya yi mulki matsayin gwamna a jihar Imo daga shekarar 2011 zuwa 2019 da laifin almundaha da almubazaranci da kudi amma ya musanta hakan.

A wani labarin daban, direbobin motoccin haya da ke bin titin Gusau zuwa Dansadau a jihar Zamfara sun shiga yajin aikin sai baba ta gani saboda yawaitar fashi da makami da garkuwa da ke yawan faruwa a hanyar, Daily Trust ta ruwaito.

Titin ya kasance wayam babu motocci tun kwanaki hudu da suka gabata domin direbobin sun ki fitowa aiki.

Shugaban kungiyar direbobi na kasa reshen Dansadau, Isihu Ticha ya shaidawa majiyar Legit.ng cewa sun shiga yajin aikin ne domin janyo hankalin mahukunta kan halin da suke ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel