Mutum 10 sun mutu, wasu 500 na asibiti bayan shan gurbataccen sinadari a Kano

Mutum 10 sun mutu, wasu 500 na asibiti bayan shan gurbataccen sinadari a Kano

- Shan wani gurbataccen sinadarin citric acid ya yi sanadin rasuwar mutum 10 a Kano yayin da wasu 500 na jinya a asibiti

- Dr Aminu Tsanyawa, kwamishinan Lafiya na jihar Kano ya sanar da hakan cikin wani sakon faifan bidiyo a ranar Alhamis

- Kwamishinan Laifyan ya gargadi mazauna Kano su yi taktsantsan da shan juice masu dauke da sinadarin citric acid musamman a watan Ramadan

Kwamishinan Lafiya na jihar Kano, Dr Aminu Ibrahim Tsanyawa ya bayyana cewa a kalla mutum 10 sun mutu sannan wasu 500 na kwance a asibiti bayan kwankwadar abin sha mai dauke da citric acid a Kano.

Ya ce 50 cikin wadanda ke jinya a asibiti na shan magunguna na ciwon koda wanda suka samu sakamakon kwankwadar abin shan, Daily Trust ta ruwaito.

Mutum 10 sun mutu, wasu 500 na asibiti bayan shan gurbataccen sinadari a Kano
Mutum 10 sun mutu, wasu 500 na asibiti bayan shan gurbataccen sinadari a Kano. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Direbobi sun shiga yajin aiki saboda fashi da makami da garkuwa a Zamfara

Kamar yadda ya fada cikin faifan bidiyo da aka raba wa manema labarai a Kano a ranar Alhamis, kwamishinan ya ce ana yi wa wadanda abin ya sha magani a asibitocin gwamnati.

Kwamishinan ya gargadi mazauna jihar game da shan 'juice' a lokacin azumin watan Ramadan.

Ya ce hukumar kiyaye hakkin masu siyan kayayyaki a Kano tana bincike a kan lamarin tana kuma shiga kasuwannin Kano farautan sinadarin.

A cikin bidiyon mai tsawon minti daya da dakika 21, ya ce: "Kamar yadda kuka sani, Ma'aikatar Lafiya a baya bayan nan ta sanar da bullar wata bakuwar cuta da aka gano shan sinadarin juice gurbatace ne ya janyo.

KU KARANTA: Gwamnonin Arewa sun yi wa Rundunar Sojoji ta'aziyyar kisar dakarunta 12 a Konshisha

"Shan jabu ko gurbatatun kaya na yi wa koda ila, da ma wasu sassan jiki masu muhimmanci."

Hukumar kare hakkin masu siyan kayayyaki tana bincike a kan lamarin tana shiga kasuwannin Kano tana kwace.

A wani labarin daban, dan majalisar tarayya, Sanata Orji Uzor Kalu ya ce ya yi imanin akwai wadanda ke yunkurin yi wa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari zagon kasa.

Dan majalisar mai wakiltan Abia North a majalisar tarayya ya yi wannan furucin ne yayin wata hira da aka yi da shi a Channels TV a ranar Litinin 12 ga watan Afirilu.

Ya ce za a magance kallubalen tsaron inda aka hada kai tsakanin gwamnatin tarayya da jihohi aka yi aiki tare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags:
Online view pixel