Hauhawar tattalin arziki ya karu zuwa 18.17%, ya jawo tashin kayan abinci

Hauhawar tattalin arziki ya karu zuwa 18.17%, ya jawo tashin kayan abinci

- Hukumar kididdiga ta fidda rahoton da ke cewa farashin kayayyaki ya karu zuwa wani adadi

- Lamarin in ji hukumar ya haifar karuwar farashin kayayyaki musamman na abinci a fadin Najeriya

- A zantawa da masanin tattalin arziki, Legit.ng Hausa ta binciko asalin abinda ake nufi da hauhawar farashi

Kididdigar farashin mabukaci, wanda ke auna kimar karuwar farashin kayayyaki da aiyuka, ya karu zuwa 18.17% a watan Maris daga 17.33% a watan Fabrairu.

Wannan ya fito ne a cikin rahoton farashi na watan Maris na 2021/rahoton hauhawar farashin kaya wanda Ofishin Kididdiga na Kasa ya fitar a ranar Alhamis.

KU KARANTA: Rashin kwarewar Buhari a mulki ne ya sa Twitter ta kai hedkwatarta Ghana, PDP

Da dumi-dumi: Hauhawar farashin kaya ya karu zuwa 18.17%, ya jawo tashin kayan abinci
Da dumi-dumi: Hauhawar farashin kaya ya karu zuwa 18.17%, ya jawo tashin kayan abinci Hoto: financialexpress.com
Asali: UGC

Hawan farashin abinci ya kuma karu da 1.16% bisa dari 100% a shekara daga 21.79% a watan Fabrairu zuwa 22.95% a watan Maris.

Wakilinmu na Legit.ng Hausa ya yi kokarin tattaunawa da wani masanin tattalin arziki, Mista Ismail Rufa'i dake aiki a kamfanin One 17 Capital Limited inda ya bayyana asalin yadda lamarin ya faru.

Da wakilinmu ya tambayi Isma'il game da abinda hauhawar farashin ke nufi. Ismail ya amsa da cewa:

"Hauhawar farashi ita ce ta ci gaba da karuwar farashi a tattalin arzikin kasa.

"Don haka, lokacin da muke da hauhawar farashi na karkara da na birni, idan muka tara duk wadannan hauhawar farashin da ake kira hauhawar farashin tattalin arziki, muna da abin da muke kira hauhawar farashin kowane wata."

"Hauhawar tattalin arziki yana nufin hauhawar farashin kayayyaki da ayyuka a tattalin arziki.

KU KARANTA: Jami'an tsaro sun dakile yunkurin balle gidan yarin Ubiaja na jihar Edo

A wani labarin, Hukumar tattara kudaden shiga ta jihar Kano (KIRS) ta ce ta rufe wasu rassa na bankin Guaranty Trust (GTBank) bisa zarginsu da kin biyan haraji, TheCable ta ruwaito.

Rassan da abin ya shafa sun hada da GTBank Kano babban reshe da ke kan hanyar Murtala Muhammad, da rassa uku a kan titin Faransa, Bachirawa, da Fagge-Wapa a cikin garin na Kano.

Garkame harabar bankin, a ranar Talata, Bashir Madobi, darektan ayyukan shari'a na hukumar tara kudaden shiga ta Kano, ya ce yanke hukuncin ya biyo bayan umarnin kotu ne kan kin bankin na biyan wasu haraji da ya kamata ga jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel