Biden ya fatattaki jakadun Rasha 10 saboda katsalandan a zabe da kutse

Biden ya fatattaki jakadun Rasha 10 saboda katsalandan a zabe da kutse

- Joe Biden, shugaban Amurka na 46 ya saka wa kasar Rasha sabbin takunkumi bisa katsalandan a zabe da kutse

- A sabon matakin da Amurka ta dauka, ta kori jakadan kasar Rasha guda 10 daga Amurka a matsayin hukunci

- Tun a shekarun baya, Amurka ta dade tana zargin Rasha da yin katsalandan a zaben tare da kutse a hukumomin gwamnati

Shugaban kasar Amurka, Joe Biden, a ranar Alhamis ya sanar da korar jakadun kasar Rasha 10 daga Amurka a yayin da kasar ke aiwatar da sabbin matakan hukunci bayan zuwan sabuwar gwamnati, The Nation ta ruwaito.

Biden ya bayyana cewa an aikata hakan ne saboda katsalandan da kasar Rasha ta yi wa Amurka yayin babban zaben shugaban kasar shekarar 2020 da kuma yi wa wasu hukumomin gwamnati kutse.

DUBA WANNAN: Direbobi sun shiga yajin aiki saboda fashi da makami da garkuwa a Zamfara

Yanzun nan: Biden ya fatattaki jakadun Rasha 10 saboda kutse katsalandan a zabe da kutse
Yanzun nan: Biden ya fatattaki jakadun Rasha 10 saboda kutse katsalandan a zabe da kutse. Hoto: TheNationNews
Asali: Twitter

Wannan takunkumin da Amurka ta saka wa Rasha ya dara wadanda tsohon shugaban kasa Barrack Obama ya yi domin hukunta Rasha saboda katsalandan a zaben kasar da kuma harar basusukan kasar na kasashen waje a cewar mutanen da aka yi hira da su kan batun.

Daga cikin wadanda aka kora daga Amurka, wasu daga cikinsu ma'aikata ne na bangaren sirri kamar yadda fadar White House ta sanar.

KU KARANTA: 'Yan Boko Haram sun kashe mutum 10 a harin da suka kai Damasak

Shugaba Biden a ranar Talata ya kira Shugaba Vladimir Putin inda ya yi bayanin cewa Amurka za ta dauki 'tsauraran matakai' domin kare kanta.

Biden ya kuma nemi kasashen biyu su gana a wata kasa na daban domin shugabannin su duba yiwuwar bangarorin da za su iya aiki tare.

Amma kakakin Kremlin (Rassa) Dmitry Peskov ya ce wannan sabbin takunkumin da Amurka ta saka mata da ya kira haramtacce ne ba zai taimaka wurin ganin taron ta yi nasara ba.

A wani labarin daban, dan majalisar tarayya, Sanata Orji Uzor Kalu ya ce ya yi imanin akwai wadanda ke yunkurin yi wa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari zagon kasa.

Dan majalisar mai wakiltan Abia North a majalisar tarayya ya yi wannan furucin ne yayin wata hira da aka yi da shi a Channels TV a ranar Litinin 12 ga watan Afirilu.

Ya ce za a magance kallubalen tsaron inda aka hada kai tsakanin gwamnatin tarayya da jihohi aka yi aiki tare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel