Rashin kwarewar Buhari a mulki ne ya sa Twitter ta kai hedkwatarta Ghana, PDP

Rashin kwarewar Buhari a mulki ne ya sa Twitter ta kai hedkwatarta Ghana, PDP

- Jam'iyyar PDP ta caccaki shugaba Buhari da jam'iyyar APC game da kai hedkwatar Twitter Ghana

- Jam'iyyar ta PDP ta zargi shugaba Buhari da rashin kwarewa a shugabanci wanda ya jawo baraka

- A cewar PDP, dasa hedkwatar ta Twitter a Ghana na da nasaba da laifukan shugaba Buhari da APC

A makon nan ne kamfanin sada zumunta ta Twitter ta sanar da dasa hedkwatarta ta Afrika a kasar Ghana, lamarin da ya jawo cece-kuce a tsakanin jama'ar Najeriya.

Jam'iyyar adawa ta PDP ta caccaki gwamnatin Buhari, tare da alakanta dasa hedkwatar ta Twitter a kasar Ghana da rashin kwarewar mulkin shugaba Buhari.

PDP ba ta bar jam'iyyar APC ba, ta kuma hada da jam'iyyar mai ci ta ce akwai laifinta a cikin lamarin kai hedkwatar Twitter din Ghana.

PDP ta bayyana cewa, lamarin ya faru duk da cewa Najeriya ta dara kasar Ghana adadin masu amfani da Twitter da kuma mamora ta fuskar kasuwanci saboda laifin APC da shugaba Buhari.

KU KARANTA: Hotunan kamfen din takarar shugaban kasa na Bukola Saraki sun cika garin Abuja

Rashin kwarewar Buhari a mulki ne ya sa Twitter ta kai hedkwatar ta Afrika Ghana, PDP
Rashin kwarewar Buhari a mulki ne ya sa Twitter ta kai hedkwatar ta Afrika Ghana, PDP Hoto: @OfficialPDPNig
Asali: Twitter

Legit.ng Hausa ta hango sanarwar da PDP ta wallafa a shafinta na Twitter cewa:

"PDP ta koka kan yadda rashin iya shugabanci na shugaba Buhari da APC suka ingiza Twitter suka dasa Hedikwatar Afirka zuwa Ghana maimakon Najeriya duk da cewa Najeriya ta fi yawan masu amfani da Twitter da kuma damar kasuwanci fiye da Ghana."

PDP ta kuma bayyana mahangarta dame da dalilan da suka sanyaTwitter fifita kasar kan Najeriya.

"Fifikon Twitter ga Ghana a kan Najeriya ya samu ne ta hanyar manufofin da ba su dace ba na tattalin arziki, kyamar danniya ga 'yancin fadar albarkacin baki, hana 'yancin amfani da bude yanar gizo da gwamnatin Buhari da APC suka yi.

"Wannan kari ne kan lalacewar ababen more rayuwa, cin hanci da rashawa da kuma gazawar fadar shugaban kasa ta Buhari da APC don magance matsalar rashin tsaro da ya jawowa kasar mu."

PDP ta kuma bayyana cewa, zabar kasar Ghana da Twitter ta yi abin alhini ne ga Najeriya tare da zama abin kunya a idon duniya.

KU KARANTA: JAMB ta soke amfani da Email a dawainiyar rajistar jarrabawarta

A wani labarin daban, Kididdigar farashin mabukaci, wanda ke auna kimar karuwar farashin kayayyaki da aiyuka, ya karu zuwa 18.17% a watan Maris daga 17.33% a watan Fabrairu.

Wannan ya fito ne a cikin rahoton farashi na watan Maris na 2021/rahoton hauhawar farashin kaya wanda Ofishin Kididdiga na Kasa ya fitar a ranar Alhamis.

Hawan farashin abinci ya kuma karu da 1.16% bisa dari 100% a shekara daga 21.79% a watan Fabrairu zuwa 22.95% a watan Maris.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.