Jami'an tsaro sun dakile yunkurin balle gidan yarin Ubiaja na jihar Edo

Jami'an tsaro sun dakile yunkurin balle gidan yarin Ubiaja na jihar Edo

- Hukumar tsaro ta NSCDC ta shawo kan wani yunkuri na balle gidan yari a jihar Edo

- Hukumar ta ce ta samu taimakon sojoji da 'yan sanda a yayin da take shawo kan rikicin

- Hakazalika ta ce wasu jami'ai sun ji raunuka a yunkurin shawo kan rikicin da ya barke

Hukumar tsaro ta NSCDC a jihar Edo, ta ce ta dakile wani yunkurin da fursunoni suka yi a cibiyar Kula da Gyaran Hali ta Najeriya (NCoS) dake Ubiaja a karamar hukumar Esan ta Kudu maso Gabas na balle gidan yari, PM News ta ruwaito.

Mista Richard Ogbebor, jami'in hulda da jama'a na rundunar a cikin wata sanarwa a Benin ya bayyana cewa yunkurin fasa gidan yarin ya faru ne daga karfe 3:00 zuwa 5:00 na yamma a ranar Laraba.

Ogbebor ya bayyana cewa, rundunar ta samu kira sannan kuma ta tura jami'anta zuwa wurin.

KU KARANTA: Rashin kwarewar Buhari a mulki ne ya sa Twitter ta kai hedkwatarta Ghana, PDP

Jami'an tsaro sun dakile yunkurin balle gidan yarin Ubiaja na jihar Edo
Jami'an tsaro sun dakile yunkurin balle gidan yarin Ubiaja na jihar Edo Hoto: theguardian.ng
Asali: UGC

Tawagar ta NSCDC ta kasance karkashin jagorancin Mista Samuel Ogbeide, Mataimakin Sufeto na rundunar ta daya.

Ogbebor ya ce lokacin da aka isa wurin, an gano cewa fursunonin sun balle daga dakunan da suke ciki kuma tuni suka shiga fada da jami’an Kula da Gyaran Halin.

Ya bayyana cewa a kokarin shawo kan rikicin wasu jami'an sun samu rauni daban-daban.

Ya ci gaba da cewa, duk da haka, tare da taimako na jami'ai daga Sojojin Najeriya, Birged ta 4, da kuma Kwaman na Edo, Rundunar 'Yan Sandan Najeriya, daga karshe an ci galaba kan fursunonin kuma an mayar da su dakunansu.

Ya kara da cewa dukkan hukumomin tsaro sun karfafa tsaro a wurin da rikicin ya barke.

KU KARANTA: Hotunan kamfen din takarar shugaban kasa na Bukola Saraki sun cika garin Abuja

A wani labarin, Baya ga makudan kudaden da ake biya a matsayin fansa ga masu satar mutane daga iyalan mutanen da aka sace, a yanzu haka ‘yan bindigan sun nemi a basu buhunan shinkafa da kayan miya a matsayin wani bangare na fansa.

Al’umomin karkara da ke yankunan Kuje, Kwali, Gwagwalada da kuma Abaji sun shaida ci gaba da kai hare-hare, inda aka sace sama da mutane 30 a cikin watanni uku da suka gabata kuma suka karbi kudin fansa na miliyoyin nairori.

Amma kwanan nan, yayin sace wasu mazauna yankin Kiyi da Anguwar Hausawa, masu garkuwar sun gaya wa iyalan wadanda suka yi garkuwar da su kawo buhunan shinkafa, taliya, supageti da kuma katan din maggi tare da kudin fansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel