JAMB ta soke amfani da Email a dawainiyar rajistar jarrabawarta

JAMB ta soke amfani da Email a dawainiyar rajistar jarrabawarta

- Hukumar JAMB ta bayyana cewa, ta soke amfani da emel wajen rajistar jarrabawa

- Ta bayyana cewa, amfani da wayar hannu kadai ya wadata dawainiyar rajistar duka

- Hakazalika ta soke karbar tsabar kudi a cibiyoyin rajistar mallakar ta a fadin kasar

Hadaddiyar Hukumar Jarrabawar Shiga Jami'a (JAMB) ta ce ba a bukatar amfani da emel yanzu don yin jarabawar shiga manyan makarantu (UTME) da kuma rajistar shiga ta kai tsaye (DE), Daily Trust ta ruwaito.

Farfesa Ishaq Oloyede, wanda ya bayyana haka lokacin da yake zantawa da manema labarai a Abuja, ya ce saboda haka, masu rubuta jarrabawar za su bi wadannan hanyoyin don samun bayanan su yayin rajistar ko bayan ta.

"Daga ranar Alhamis, 15 ga Afrilu, 2021, ba za a sake bukatar masu rubuta jarrabawa su samar da emel ba yayin rajista."

“Amfani da manhajar wayar hannu na masu rubuta jarrabawar ko kuma latsa 55019 (da aka tsara) misali duba sakamakon shiga, za a yi amfani da shi wajen rajista, shiga, da sauransu a kan bayanansu.

KU KARANTA: Hotunan kamfen din takarar shugaban kasa na Bukola Saraki sun cika garin Abuja

JAMB ta soke amfani da Email a dawainiyar rajistar jarrabawarta
JAMB ta soke amfani da Email a dawainiyar rajistar jarrabawarta Hoto: theguardian.ng
Asali: UGC

"Ana iya cire takardar zana jarrabawa (Fadakarwa) ko kuma sakamakon jarrabawar ko kuma tikiti a ko ina ta amfani da lambar rajistar JAMB kawai," in ji shi.

Ya yi bayanin cewa masu rubuta jarrabawar za su bayar da adireshinsu na emel ne kawai bayan an gabatar da aikin rajistar na 2021 UTME/DE idan JAMB ta rufe ta manhajar waya a wayar da aka yi rijista.

Hakanan, aikawa da kalmar emel (a bar sarari sannan adireshin emel) a kan wayar da aka yi rijista zuwa 55019.

"Za a rubuta emel sau biyu don daidaito (Za a shigar da adiresoshin emel sau biyu don ingantawa da kuma hana kuskuren rubutu," in ji Oloyede.

Shugaban JAMB din ya ce sabon tsarin shi ne tabbatar da cewa bayanan masu rubuta jarrabawar sun tsira daga damfara a yanar gizo da sauran masu aikata laifuka wadanda a yayin rajistar UTME/DE suke satar lambar sirri ta emel don aikata magudi.

Shugaban na JAMB ya ce wayar hannu ta mutum a yanzu ta kasance ita ce kadai babbar kayan aiki da za ta aiwatar da dukkan ayyukan rajistar.

Da yake ci gaba da magana, Oloyede ya ce Hukumar ta daina amfani da tsabar kudi don duk wata ma'amala a cibiyoyin jarrabawa na Kwamfuta (CBT) mallakar JAMB, yana mai cewa kawai ana amfani da katuna na ATM ne don biya.

Ya kuma bada dama ga wadanda ba zasu iya ba da su ziyarci cibiyoyin rajista masu zaman kansu don yin rajistar.

KU KARANTA: Matar gwamnan Zamfara ta tabbatar da nadin membobin Miyetti Allah 20 a gwamnati

A wani labarin, Hadaddiyar Hukumar Jarrabawar Shiga Jami'a (JAMB) ta sanya Jami'ar Abuja (UniAbuja) a cikin cibiyoyin da ke gudanar da bada guraben shiga ba bisa ka'ida ba.

A wata sanarwa, Shugaban, Hulda da Jama'a na JAMB, Fabian Benjamin a ranar 13 ga watan Afrilu, ya ce jami'ar na daga cikin cibiyoyin da ke ba da guraben shiga ga dalibai ba tare da sanin hukumar ba.

Ya ce: "Sakamakon haka, irin wadannan guraben shiga sun saba doka, ba za a karbesu ba kuma ya saba wa dokoki da ka’idoji da ke jagorantar shiga manyan makarantu a Najeriya kamar yadda Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta amince kuma aka bayar a CAPS.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel