Hukumar haraji ta Kano ta garkame GTBank kan kin biyan haraji

Hukumar haraji ta Kano ta garkame GTBank kan kin biyan haraji

- Gwamnatin jihar Kano ta garkame Bankin Guaranty Trust na jihar bisa kin biyan haraji ga jihar

- Hukumar harajin ta maka bankin a kotu kan kin biyan harajin da ya dace ya biya jihar ta Kano

- Bayan garkame bbankin, hukumar harajin ta bayyana cewa, akwai kuma tara da zai biya baya ga harajin

Hukumar tattara kudaden shiga ta jihar Kano (KIRS) ta ce ta rufe wasu rassa na bankin Guaranty Trust (GTBank) bisa zarginsu da kin biyan haraji, TheCable ta ruwaito.

Rassan da abin ya shafa sun hada da GTBank Kano babban reshe da ke kan hanyar Murtala Muhammad, da rassa uku a kan titin Faransa, Bachirawa, da Fagge-Wapa a cikin garin na Kano.

Garkame harabar bankin, a ranar Talata, Bashir Madobi, darektan ayyukan shari'a na hukumar tara kudaden shiga ta Kano, ya ce yanke hukuncin ya biyo bayan umarnin kotu ne kan kin bankin na biyan wasu haraji da ya kamata ga jihar.

KU KARANTA: Zan ci gaba da addu'a Allah yasa Musulmai su ginawa kiristoci Coci, Bishop Kukah

Hukumar haraji ta Kano ta garkame GTBank kan kin biyan haraji
Hukumar haraji ta Kano ta garkame GTBank kan kin biyan haraji Hoto: nairametrics.com
Asali: UGC

“Don haka bin umarnin kotu ne, Babbar Kotun Jihar Kano ta ba da umarnin gwajin abin da muka gabatar kuma mun samu hukunci.

"Shi ya sa muka je wurin domin aiwatar da hukuncin kotun da kuma tilasta biyan harajin da ya kamata kamar yadda aka tanada a karkashin abinda ya gabata na dokokin kudaden shiga,” in ji shi.

“Zamu tattara sama da Naira biliyan daya daga bankin. Muna fatan su zo su zauna tare da mu domin mu san matakin da za mu dauka don nuna cewa a shirye suke su sasanta da mu don mu sasanta batun.

“Amma abin da ya kawo mana cikas daga daukar wannan matakin shi ne, tun farko mun nemi wasu takardu daga wurinsu wanda suka kasa girmamawa su ba mu takardun don haka ne ya sa muka shigar da kara a gaban kotu.

"Amma har yanzu muna neman takardun. Dangane da wadannan takaddun, zamu iya tantance ainihin adadin abin da ya kamata a biya gwamnatin Kano.

“Dole ne su biya 25% na jimillar abin da ke kanmu kuma dole ne su kawo mana takardun da muka nema a baya.

"Har ila yau, akwai tarar 10% cikin 100% ga duk wani mai biyan haraji kan harajin da ya dace. Yana daga cikin abin da ake nema a gaban kotu cewa su biya 10% cikin 100%.”

A wani labarin, A safiyar yau ne NewsWireNGR ta buga cewa, gwamnatin kasar Amurka ta sanya sunan Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Dr Isa Ali Ibrahim Pantami cikin jerin masu hannu cikin tashin tashina na Boko Haram.

Bayan da jaridar ta lashe amanta biyo bayan cece-kuce, ta bayyana janye labarin da ta fitar, amma Dr Isa Ali Pantami ya mai da martani kan rubutun da jaridar ta wallafa.

Ya rubuta a shafinsa na Tuwita cewa: "@NewsWireNGR Janye rubutunku ta hanyar binciken ka mai zaman kansa, na lura dashi. Ko da yake, aikin jarida na bincike yana bukatar bincike kafin a buga shi, ba bayan an buga ba.

KU KARANTA: Sakon Buhari ga Musulmai a Ramadana: Ku guji a ingizaku zuwa raba kawunanku

Asali: Legit.ng

Online view pixel