'Yan fashin intanet sun yi wa JAMB kutse, sun sace miliyoyin naira
- Hukumar JAMB ta ce wasu yan fashin intanet sun kutsa shafinta sun karkatar da fiye da Naira miliyan 10
- Shugaban hukumar, Farfesa Ishaq Oloyede ne ya bayyanawa manema labarai hakan babban birnin tarayya Abuja
- Oloyede ya ce an yi nasarar kama wadanda suka yi kutsen cikinsu har da wani Sahabi Zubairu da ya karkatar da fiye da N400,000
Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Makarantun Gaba da Sakandari, JAMB, ta ce yan fashin intanet sun kutsa shafinta sun sauya sunayen wasu ma'aikatan wucin gadi da ta dauka, The Cable ta ruwaito.
Ishaq Oloyede, shugaban JAMB, yayin jawabin da ya yi wa manema labarai a Abuja ya ce an sace fiye da Naira miliyan 10 cikin kudin da ya kamata a biya ma'aikatan na wucin gadi.
DUBA WANNAN: 2023: Hotunan Neman Takarar Shugaban Ƙasa na Saraki Sun Mamaye Abuja
A cewarsa, hukumar ta gano kutsen da aka yi bayan bincike mai zurfi da ta yi, hakan yasa aka yi nasarar kama wani Sahabi Zubairu a jihar Taraba da wasu daban.
Ya ce tsarin gwamnati ne a rika biyan ma'aikatan wucin gadin kudinsa kai tsaye zuwa asusun ajiyar bankunansu hakan kuma shine ya haifar da wannan kalubalen.
Kazalika, ya ce sashin kula da kudade na hukumar ita ma bata tantance sunayen da asusun bankunan ba kafin ta tura kudaden wadanda aka lissafa sunayensu a shafin hukumar.
Shugaban na Boss ya ce tuni dai an biya ma'aikatan wucin gadin kudadensu inda ya bada tabbacin cewa za a kwato kudaden daga wadanda suka sace sannan a mika su hannun hukumar EFCC.
KU KARANTA: Yadda miji ya kashe babban limami bayan kama shi zigidir da matarsa a gidan maƙwabta
Wanda ake zargin, Zubairu ya ce wani Samuel Tanko ne ya koya masa damfarar kuma shima ya koya wa kimanin mutum 12 wasu ma yan uwansa ne.
Ya kara da cewa ya samu fiye da N400,000 da aka karkatar zuwa asusun ajiyarsa na banki. Wani Nasiru Mohammed ya ce ya samu N220,000 yayin da wasu suka samu tsakanin N286,000 zuwa N440,000.
A wani labarin daban, dan majalisar tarayya, Sanata Orji Uzor Kalu ya ce ya yi imanin akwai wadanda ke yunkurin yi wa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari zagon kasa.
Dan majalisar mai wakiltan Abia North a majalisar tarayya ya yi wannan furucin ne yayin wata hira da aka yi da shi a Channels TV a ranar Litinin 12 ga watan Afirilu.
Ya ce za a magance kallubalen tsaron inda aka hada kai tsakanin gwamnatin tarayya da jihohi aka yi aiki tare.
Asali: Legit.ng