'Yan bindiga sun kashe masunci a sabon harin da suka kai a Kaduna

'Yan bindiga sun kashe masunci a sabon harin da suka kai a Kaduna

- 'Yan bindiga sun halaka wani masunci a karamar hukumar Zangon Kataf a Kaduna

- Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na Kaduna, Mista Samuel Aruwan ya tabbatar da hakan

- Mr Aruwan ya ce an fara bincike kan kisar da nufin gano wadanda suka aikata domin su girbi abinda suka shuka

'Yan bindiga sun kashe wani masunci, Adamu Bala, a yayin da ya tafi rafi kama kifi a tsakanin Zango da Ungwan Ruhogo a karamar hukumar Zangon Kataf na jihar Kaduna, The Punch ta ruwaito.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Mista Samuel Aruwan, ya tabbatar da harin inda ya ce lamarin ya faru ne a ranar Litinin amma bai bada karin bayani ba.

'Yan bindiga sun kashe masunci a sabon harin da suka kai a Kaduna
'Yan bindiga sun kashe masunci a sabon harin da suka kai a Kaduna. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: El-Rufa'i ya umurci cocin RCCG ta cigaba da baza rassa a faɗin jihar Kaduna

Kwamishinan ya ce, "Dakarun Operation Safe Haven sun ruwaito kisa tsakanin Zango da Ungwan Ruhogo a karamar hukumar Zangon Kataf a jihar.

"A cewar rahoton, wasu mutanen da ba a sani ba sun kashe wani Adamu Bala bayan ya tafi rafi kama kifi a ranar Litinin 12 ga watan Afrilun 2021.

"An tsinci gawarsa a gabar rafi a jiya Talata 13 ga watan Afrilun shekarar 2021.

KU KARANTA: Yadda miji ya kashe babban limami bayan kama shi zigidir da matarsa a gidan maƙwabta

"Gwamna Nasir El-Rufai ya yi bakin samun rahoton kuma ya yi wa iyalan wanda ya rasu ta'aziyya sannan ya yi addu'ar Allah ya jikan marigayin ya gafarta masa.

"A halin yanzu an fara bincike a kan lamarin."

A wani labarin daban, dan majalisar tarayya, Sanata Orji Uzor Kalu ya ce ya yi imanin akwai wadanda ke yunkurin yi wa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari zagon kasa.

Dan majalisar mai wakiltan Abia North a majalisar tarayya ya yi wannan furucin ne yayin wata hira da aka yi da shi a Channels TV a ranar Litinin 12 ga watan Afirilu.

Ya ce za a magance kallubalen tsaron inda aka hada kai tsakanin gwamnatin tarayya da jihohi aka yi aiki tare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel