Yanzu-Yanzu: Buhari ya naɗa wadda ta rubuta littafi kan Aisha muƙami a UNESCO

Yanzu-Yanzu: Buhari ya naɗa wadda ta rubuta littafi kan Aisha muƙami a UNESCO

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Mrs Hajo Sani matsayin jakadiyar Nigeria a UNESCO

- Wannan nadin na zuwa ne kasa da sati daya bayan kaddamar da littafin da ta rubuta kan mai dakin shugaban kasa, Aisha Buhari

- Baya ga nadin Hajo Sani, shugaban kasar ya kuma yi wasu sabbin nade-nade a bangarorin ilimi guda shida

Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Mrs Hajo Sani, wacce ta rubuta littafin a kan matarsa a matsayin jakadiyar Nigeria na dindindin a Hukumar Kyautata Ilimin Kimiyya da Al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya wato UNESCO, rahoton Daily Trust.

Wannan nadin na zuwa ne kasa da mako daya bayan kaddamar 'Aisha Buhari: Being Different', littafin da ta rubuta a kan First Lady Aisha Buhari da aka kaddamar da fadar shugaban kasa a Abuja.

DUBA WANNAN: Yadda miji ya kashe babban limami bayan kama shi zigidir da matarsa a gidan maƙwabta

Yanzu-Yanzu: Buhari ya naɗa wadda ta rubuta littafi kan Aisha muƙami a UNESCO
Yanzu-Yanzu: Buhari ya naɗa wadda ta rubuta littafi kan Aisha muƙami a UNESCO. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

Bayan Hajo Sani, Buhari ya kuma yi wasu nade-nade masu muhimmanci a bangaren ilimi.

Ben Bem Goong, Direktan sashin watsa labarai da hulda da mutane, ya tabbatar da nadin a cikin wata sanarwa.

Ga sauran nade-naden:

KU KARANTA: 2023: Hotunan Neman Takarar Shugaban Ƙasa na Saraki Sun Mamaye Abuja

  • Farfesa John Okpako Enaohwo, shugaban kwamiti na kasa na kwallejojin Ilimi, NCCE, Abuja.
  • Farfesa Abdullahi A. Abba, Shugaba a kwamitin Kwalejojin Tarayya na Kimiyyar Lafiya, Otukpo, jihar Benue.
  • Farfesa Idris Muhammad Bugaje, Babban sakatare, Hukumar Ilimin Fasaha na Kasa, NBTE, Kaduna.
  • Dr. Benjamin Ogbole Abakpa, babban sakatare na Hukumar Ilimin Babban Sakandare, NSSEC, Abuja.
  • Farfesa Paulinus Chijikoke Okwelle, Babban sakatare, Hukumar Kwalejojin Ilimi na Kasa, NCCE, Abuja.
  • Farfesa Ibrahim Muhammad a matsayin direkta, Cibiyar Ilimin harshen larabci, Ngala, Jihar Borno.

A wani labarin daban, dan majalisar tarayya, Sanata Orji Uzor Kalu ya ce ya yi imanin akwai wadanda ke yunkurin yi wa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari zagon kasa.

Dan majalisar mai wakiltan Abia North a majalisar tarayya ya yi wannan furucin ne yayin wata hira da aka yi da shi a Channels TV a ranar Litinin 12 ga watan Afirilu.

Ya ce za a magance kallubalen tsaron inda aka hada kai tsakanin gwamnatin tarayya da jihohi aka yi aiki tare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel