Shekaru 7 Kenan, Muna Buƙatar mu haɗu da 'ya'yan mu Kafin mu mutu, Iyayen Ɗaliban Chibok Sun roƙi FG

Shekaru 7 Kenan, Muna Buƙatar mu haɗu da 'ya'yan mu Kafin mu mutu, Iyayen Ɗaliban Chibok Sun roƙi FG

- Iyayen sauran ɗalibai mata da mayaƙan Boko Haram suka sace kimanin shekaru bakwai kenan, sun ce suna son ganin yayan su kafin su bar Duniya

- A yau 14 ga watan Afrilu 2021, aka cika shekaru bakwai da ɗauke yan matan makarantar Chibok ɗin wanda aka yi a rana mai kamar ta yau a shekarar 2014.

- Iyayen sun roƙi gwamnatin tarayya data taimaka ta ceto musu yayan su don aƙalla su gana kafin rayuwarsu ta ƙare

Iyayen ragowar ɗalibai mata 112 da aka sace a makarantar sakandiren mata dake Chibok jihar Borno, sun bayyana cewa suna son ganin yayan su kafin su mutu.

Tunda mayaƙan Boko Haram dake biyayya ga Abubakar Sheƙau suka sace yayan nasu, wasu daga cikin iyayen sun rasu saboda tashin hankali wasu kuma sun rasu saboda lokaci yayi.

KARANTA ANAN: Bayani Dalla-Dalla: Rukunin Mutane 3 da suka cancanci su sami bashi daga CBN na Kuɗin COVID19

Waɗanda har yanzun suke raye sun bayyana cewa suna da yaƙinin yayan su na raye don haka suna kira ga gwamnati ta taimaka ta kuɓutar dasu.

Yau shekara bakwai kenan dai-dai tun sanda mayaƙan Boko Haram ɗin suka kai farmaki GGSS Chibok ranar 14 ga watan Afrilu, 2014.

Kuma suka tilasta ma ɗalibai 276 shiga babbar mota sannan suka tafi da su Dajin Sambisa kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

A hanyar tafiya da su dajin ne wasu daga cikin ɗaliban suka rinƙa maƙale wa a Bishiyoyi suna komowa gida amma wasu basu samu wannan nasarar ba.

Shekaru 7 Kenan, Muna Buƙatar mu haɗu da 'ya'yan mu Kafin mu mutu, Iyayen Ɗaliban Chibok Sun roƙi FG
Shekaru 7 Kenan, Muna Buƙatar mu haɗu da 'ya'yan mu Kafin mu mutu, Iyayen Ɗaliban Chibok Sun roƙi FG Hoto: @Thecableng
Asali: Twitter

Amma duk da haka bayan kuɓutar wasu, da kuma sakin wasu da maharan suka yi bayan tattaunawa ta tsawon lokaci, dayawa daga cikin ɗalibai 107 da suka koma gidajen su na fama suga sun dawo dai-dai kamar da.

KARANTA ANAN: A karon farko, Gwamnan Nasarawa ya rantsar da mace a matsayin babbar Alkalin jihar

Wasu daga cikin su an kai su amurka sun kammala karatun jami'a, wasu kuma har yanzun sun ma kasa samun nasara a jarabawar fita daga sakandire.

Tun shekarun baya da suka wuce, 14 ga watan Aprilu, 2016. Ƙungiyar iyayen matan Chibok da aka sace sun rasa mambobin su guda 17.

Da yawa daga cikinsu sun rasu ne a wani yanayi da yake da alaƙa da tashin hankali bayan dogon jira batare da sunga yayan nasu ba kuma babu wani sahihin bayani game da su.

A wani labarin kuma Bayani Dalla-Dalla kan Yanda zaka yi rijistar JAMB 2021 ba tare da samun Matsala ba

Hukumar dake shirya jarabawar share fagen shiga makarantun gaba da sakandire JAMB ta sanar da fara sayar da fom ranar Asabar ɗin da ta gabata.

JAMB ta dakatar da fara yin rijistar ne tun baya saboda wasu matsaloli da ba'a yi tsammani ba a kan lambar zama ɗan ƙasa NIN.

Asali: Legit.ng

Online view pixel