A karon farko, Gwamnan Nasarawa ya rantsar da mace a matsayin babbar Alkalin jihar

A karon farko, Gwamnan Nasarawa ya rantsar da mace a matsayin babbar Alkalin jihar

- Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya rantsar da mace mai suna Aisha Bashir Aliyu a matsayin shugabar alƙalai (CJ)

- Aisha dai ta zama ita ce mace ta farko a jihar da zata riƙe wannan babban muƙami, wanda hakan ya zama babban ƙalubale a gabanta musamman tazo dai-dai lokacin da ma'aikatan shari'a ke yajin aiki

- Gwamna Sule ya roƙi ma'aikatan da su dubi girman Allah su koma bakin aikin su, su janye wannan yajin aikin da suke yi

Gwmnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya rantsar da Aisha Bashir Aliyu a matsayin babbar alƙali jihar.

KARANTA ANAN: Yan Bindiga sun kai hari wata Kasuwa a jihar Neja, sun kashe yan Bijilanti Biyar

Aisha ta zama mace ta farko a tarihin jihar da ta riƙe wannan babban muƙamin na shugabar alƙalai (CJ) a jihar Nasarawa.

Wannan na ƙunshe ne a wani jawabi da gwamnatin jihar ta saki a shafinta na dandalin sada zumunta Tuwita.

Jim kaɗan bayan rantsar da CJ ɗin ta jihar, gwamnan ya ce gwamnatinsa ta ɗauki ɓangaren shari'a da matuƙar muhimmanci kuma zata cigaba da samar ma ɓangaren duk abinda yake buƙata don tabbatar da zumuncin dake tsakaninsu.

Ya kuma ƙara da cewa gwamnatin sa zata cigaba da goyon bayan ɓangaren shari'a domin a rinƙa saurin zartar da hukunci.

A Karon farko, Gwamnan Nasarawa ya rantsar da mace a matsayin babbar Mai Shai'a ta jihar
A Karon farko, Gwamnan Nasarawa ya rantsar da mace a matsayin babbar Mai Shai'a ta jihar Hoto: @Nasarawagovt
Asali: Twitter

KARANTA ANAN: Yanzu Yanzu: Gwarazan Sojoji na can suna fafatawa da yan bindiga a iyakar Ebonyi Da Benuwai

Sule ya kuma roƙi mambobin ƙungiyar masu shari'a da suka shiga yajin aiki da su taimaka su koma bakin aikin su.

Hakanan gwamnan ya kira yi sabuwar CJ ɗin data ɗauki muƙaminta a matsayin babban kalubale kasan cewar ita ce mace ta farko da ta rike muƙamin.

A wani ɓangaren kuma gwamnan jihar ta Nasarawa ya rantsar da Barista Muhammad Sani Bawa a matsayin shugan hukumar dake kula da ƙananan hukumomin jihar.

Gwamnan ya yi waɗannan muhimman naɗe-naɗen ne a cikin gidan gwamnatin jihar Ranar Litinin.

A wani labarin kuma Bayani Dalla-Dalla kan Yanda zaka yi rijistar JAMB 2021 ba tare da samun Matsala ba

Hukumar dake shirya jarabawar share fagen shiga makarantun gaba da sakandire JAMB ta sanar da fara sayar da fom ranar Asabar ɗin da ta gabata.

JAMB ta dakatar da fara yin rijistar ne tun baya saboda wasu matsaloli da ba'a yi tsammani ba a kan lambar zama ɗan ƙasa NIN.

Asali: Legit.ng

Online view pixel