Mataimakin Gwamna ya tsere da motocin Gwamnati 4 watanni 2 da barin kujerar mulki
- Ana zargin tsohon mataimakin gwamnan Ondo da yin gaba da motocin Gwamnati
- Har yanzu wasu motoci su na hannun Agboola Ajayi duk da ya bar ofis a kwanaki
- Gwamnan jihar Ondo ya sanar da ‘Yan Sanda su karbe kayan da ke hannun Ajayi
Gwamnatin jihar Ondo ta fada wa ‘yan sanda su tursasa wa Mista Agboola Ajayi ya dawo da wasu motocin gwamnati da ke hannunsa har yanzu.
Daily Trust ta fitar da rahoto cewa har gobe akwai motocin gwamnati da su ke hannun tsohon mataimakin gwamnan jihar Ondo, Agboola Ajayi.
Agboola Ajayi ya yi mulki tare da Mai girma gwamna Rotimi Akeredolu, amma aka samu sabani a karshen wa’adin farko, hakan ya sa aka raba gari.
KU KARANTA: Ana musayar kalamai tsakanin Kungiyar CAN da NSCIA
A wata wasika da wani Hadimin gwamnan Ondo, Dr. Doyin Odebowale, ya aika wa kwamishinan ‘yan sanda, ya ce Ajayi ya na rike da wasu motoci hudu.
Mai ba gwamnan jihar Ondo shawara kan dabaru da harkokin musamman ya zargi wadanda su ka rike mukamai a da, da cigaba da rike kayan gwamnati.
Doyin Odebowale ya sanar da ‘yan sanda cewa an yi kokarin ganin Ajayi ya dawo da kayan gwamnatin da su ke hannunsa, amma hakan ya faskara.
“Ofishinmu ya na da daurin-gindin gwamnan Ondo, Oluwarotimi Akeredolu, SAN, na karbe duk kayan gwamnati da su ke hannun wadanda su ka rike mukamai.”
KU KARANTA: Kisan da ake yi wa ‘Yan Arewa ya jawo mutane su na yin kaura
Wasikar ta ce wannan mataki da aka dauka ya shafi musamman wadanda su ka yi aiki a gwamnatin da ta shude, daga ciki har da su Mista Agboola Ajayi.
Odebowale ya ce ana so a dawo da motocin domin mataimakin gwamna mai-ci ya samu na-hawa. Motocin su ne: Land Cruiser SUV, da wasu sababbin Toyota Hilux.
Bayan shekaru kusan 30, kun ji cewa Olusegun Obasanjo ya bayyana dalilin Sojoji na kashe zaben 1993, ya ce bakin-ciki ya hana a kyale Abiola ya zama Shugaban kasa.
Da an kyale wannan zabe, da Mashood Abiola ya zama Shugaban Najeriya a 1993. Obasanjo ya bayyana wannan a lokacin da wata kungiya ta karrama shi a Abeokuta.
Asali: Legit.ng