Gwamnonin Arewa 6 Zasu haɗa ƙarfi-da-ƙarfe Wajen yaƙar yan Ta'adda a Yankunan su
- Wasu gwamnoni shida daga Arewa zasu haɗa hannu domin kawar da ta'addanci a jihohin su
- Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ne ya bayyana haka amma bai faɗi sunayen sauran gwamnoni biyar ɗin da zasu yi haɗakar da su ba
- Gwamnan ya shawarci yan ta'addan dake waɗannan jihohi da su canza kansu zuwa mutanen kirki, domin gwamnati ba zata zuba ido tana kallon su suna aika-aika a waɗannan jihohin ba
Gwamnonin shida da suka fito daga arewa zasu haɗa hannu domin kawar da matsalar tsaro da ta addabi yankunan su kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Lokaci ya yi da zamu koma ga Allah, Mu baiwa Talakawa saɗaƙa a watan Ramadana, Inji Atiku
Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, shi ne ya bayyana haka a jiya yayin da yake miƙa takardar shaidar zama Sarki ga sabon Sarkin masarautar Kagara, Ahmed Garba Gunna.
An zaɓi Ahmed Garba Gunna a matsayin sarkin kagara bayan rasuwar tsohon sarkin kuma shine sarki na biyu da zai jagoranci masarautar.
Duk da cewa gwamna Bello bai bayyana sunayen sauran gwamnonin da zasu yi wannan haɗin gwuiwar ba amma ya ƙara da cewa:
"Dukkan mu mun amince mu haɗa ƙarfi-da-karfe mu yaƙi duk wasu yan ta'adda a jihohin mu."
Gwamna Bello ya baiwa yan ta'addan dake waɗannan yankin shawarar da su canza ɗabi'unsu su zama mutanen kirki Saboda hakan zaifi musu, tun kafin su fuskanci hukuncin mutane da gwamnati.
KARANTA ANAN: Dalilin da yasa Sheikh Isa Pantami ya yi Muƙabala da Tsohon shugaban Boko Haram - Lauya
Jihar Neja dai na fuskantar matsalolin rashin tsaro iri daban-daban, Inda ɗaruruwan yan bindiga ke yawan kai hari ƙauyuka suna kashe mutane, su cinna ma wurare wuta sannan kuma su yi awon gaba da mutane.
Idan zaku iya tunawa, a jihar Neja ne wasu yan bindiga suka kai hari makarantar sakandiren gwamnati dake Kagara, inda ɗalibi ɗaya ya rasa ransa kuma suka tafi da wasu ɗaliban da yawa. Kafin daga baya su sako su bayan rahotanni sun tabbatar da an biya kuɗin fansa.
A wani labarin kuma Wasu Yan Bindiga sun sake kai hari ofishin 'Yan sanda a Cross Rivers
Wasu Yan bindiga sun sake kai hari a ofishin yan sanda a jihar Cross Rivers, sun kwace bindiga guda ɗaya ƙirar AK-47 a hannun wani ɗan Sanda
Wannan harin shine karo na uku da yan bindiga suka kai kan 'yan sandan jihar Cross Rivers cikin watanni biyu kacal.
Asali: Legit.ng