Wasu Yan Bindiga sun sake kai hari ofishin 'Yan sanda a Cross Rivers

Wasu Yan Bindiga sun sake kai hari ofishin 'Yan sanda a Cross Rivers

- Wasu Yan bindiga sun sake kai hari a ofishin yan sanda a jihar Cross Rivers, sun kwace bindiga guda ɗaya ƙirar AK-47 a hannun wani ɗan Sanda

- Wannan harin shine karo na uku da yan bindiga suka kai kan 'yan sandan jihar Cross Rivers cikin watanni biyu kacal

- Mataimakin kakakin yan sandan jihar ya tabbatar da faruwar lamarin amma ya ce hukumar su na gudanar da bincike kan harin

Wasu yan bindiga da ba'a gane ko su waye ba sun kai hari ofishin yan sanda a Cross Rivers Kamar yadda jaridar PM News ta ruwaito.

Rahotanni sun tabbatar da kai harin kuma sun bayyana cewa yan bindigar sun yi awon gaba da bindiga guda ɗaya kirar AK-47.

KARANTA ANAN: Bamu san an buga sabbin Kuɗi a watan Maris ba, CBN da Ma'aikatar kuɗi sun maida Martani

An kai harin ne a ofishin yan sanda dake Ekori ƙaramar hukumar Yahuu a jihar ta Cross Rivers.

Yan bindigar da suka kai hari ofishin, suna ɗauke da manya-manyan makamai kuma suka tsorata ɗan sandan dake aiki a lokacin ya gudu.

Sannan kuma sun yi wa wani ɗan sanda guda ɗaya dukan tsiya kafin daga bisani su ƙwace bindigarsa AK-47 su tafi da ita.

Wannan harin da aka kai yasa aka kulle ofishin yan sandan na Ekorihar sai baba-ta-gani.

Wasu Yan Bindiga sun sake kai hari ofishin 'Yan sanda a Cross Rivers
Wasu Yan Bindiga sun sake kai hari ofishin 'Yan sanda a Cross Rivers Hoto: @pmnewsnigeria
Asali: Twitter

Hukumar yan sandan jihar ta umarci jami'an dake aiki a wajen su koma hedkwatar hukumar ta ƙaramar hukumar Yahuu.

Wannam farmakin shine karo na uku da aka kai ofishin yan sanda a jihar Cross Rivers cikin watanni biyu kacal.

KARANTA ANAN: Sarkin Musulmi Ya umarci al'umar Musulmi su nemi jinjirin watan Ramadan ranar Litinin

Yan bindiga sun kai harin farko ne a wajen duba ababen hawa dake kan hanyar Idundu a Calabar, inda aka kashe jami'ai biyu.

An kai hari na biyun ne a garin Obubra Inda dayawan jami'an yan sanda haɗe da sojoji suka rasa rayukansu.

Mataimakin Kakakin hukumar yan sandan jihar, Igri Ewa, ya tabbatar da faruwar Lamarin.

Ya ce Rundunar 'yan sandan na cigaba da gudanar da bincike, kuma zata bayyana binciken da ta yi da zarar ta gama.

A wani labarin kuma APC ta raba kayan Abinci cike da Manyan Motocin ɗaukar kaya 130 ga talakawa Saboda Ramadan

Jami'iyyar APC ta raba kayan abinci cike da manyan motocin ɗaukar kaya 130 ga talakawa da mabuƙata a jihar Zamfara

Tsohon gwamnan jihar, Abdul'aziz Yari ne ya bayyana hakaa Gusau, babban birnin jihar, lokacin da jam'iyyar ta ƙaddamar da fara rabon kayan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel