Da duminsa: Mutane da dama sun jikkata sakamakon fashewar tunkunyar gas a Legas

Da duminsa: Mutane da dama sun jikkata sakamakon fashewar tunkunyar gas a Legas

- Tunkunyar iskar gas ta fashe ta yi 'bindiga' a Agboju a jihar Legas

- Rahotanni sun bayyana cewa mutane da dama sun jikkata sakamakon fashewar

- Hukumar LASEMA ta jihar Legas ta tabbatar da afkuwar lamarin kuma ta tura jam'anta

An samu fashewar gas a karamar hukumar Amuwo-Odofin na jihar Legas a ranar Talata 12 ga watan Afrilun shekarar 2021, The Punch ta ruwaito.

An gano cewa mutane da dama sun jikkata sakamakon lamarin da ya faru a layin Iyasoko da ke Agboju, Amuwo-Odofin.

DUBA WANNAN: Yadda miji ya kashe babban limami bayan kama shi zigidir da matarsa a gidan maƙwabta

Labari da duminsa: Bututun Iskar Gas Ta Yi 'Bindiga' a Legas
Labari da duminsa: Bututun Iskar Gas Ta Yi 'Bindiga' a Legas. Hoto: @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

An ruwaito cewa lamarin ya faru ne misalin karfe 6.55 na yamma.

Mai magana da yawun hukumar bada agajin gaggawa na Legas, LASEMA, Nosa Okunbor ya tabbatar da fashewar gas din inda ya ce an tura jami'ai masu ceto zuwa wurin misalin karfe 6.50 na yamma.

KU KARANTA: Tsohon gwamna ya fallasa shirin zagon ƙasa da ake yi wa gwamnatin Buhari

Ba a tantance adadin mutanen da goborar ta shafa ba a lokacin hada wannan rahoton.

Ya ce, "Eh, da gaske ne. Tawagar jami'an mu suna hanyarsu na zuwa wurin. Cinkoson ababen hawa ne ya sa suka yi jinkiri. Ba zan iya tantance irin barnar da ta faru ba a yanzu."

A bangare guda kun ji cewa shahararren Malamin Addinin Musulunci, Sheikh Muhammad Nuru Khalid, ya yi ikirarin cewar wadansu daga cikin masu fada-a-ji wanda ya hada da 'yan siyasa da Malaman addini, su ne asalin ma su daukar nauyin rashin tsaro a wasu sassa na kasar nan .

Ya yi wannan bayani ne a Abuja a yayin kaddamar da wata littafi da aka wallafa kamar yadda Vangaurd ta ruwaito.

Khalid ya yi ikirarin cewar 'yan ta'adda wanda da yawansu matasa ne su na aikata ta'addanci ga al'umma sakamakon mu'amalarsu da sanannu malamai da 'yan siyasa wadanda su ke son kasar ta kone kurmus.

Asali: Legit.ng

Online view pixel