Ku tuhumi magabatana a kan kudin makamai ba ni ba, COAS ga majalisar tarayya

Ku tuhumi magabatana a kan kudin makamai ba ni ba, COAS ga majalisar tarayya

- Tattaunawa tsakanin shugaban sojin saman Najeriya da 'yan kwamitin majalisar wakilai kan makamai ta dauka zafi

- Shugaban sojin kasan ya ki yi wa 'yan majalisar karin bayani kan takardun da ya mika gabansu inda yace komai a takaice yake

- Ya bukaci 'yan majalisar da su daina tuhumarsa da batun makamai, su nemi magabatansa don sun fi shi sanin inda suke

Lamari ya dauka zafi tsakanin wasu 'yan kwamitin rikon kwarya na majalisar wakila a kan makamai, da shugaban sojin kasa, Laftanal janar Ibrahim Attahiru bayan bincike a kan siyan makamai na sojin Najeriya.

Lamarin ya juya yayin da shugaban sojin kasan ya ki kara bayani kan wasu takardu da ya mika gaban kwamitin inda yace su duba takardun da kansu domin babu wani karin bayani.

Shugaban sojin ya jaddada cewa bai dade da hawa kujerarsa ba don haka ba shi ke da hakkin yin magana a kan makaman da magabatansa suka siya ba, Channels Tv ta wallafa.

KU KARANTA: Da duminsa: Fulani makiyaya sun kai hari yankin Ngbo dake Ebonyi

Ku tuhumi magabatan a kan kudin makamai ba ni ba, COAS ga majalisar tarayya
Ku tuhumi magabatan a kan kudin makamai ba ni ba, COAS ga majalisar tarayya. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

"Takardun dake gabanku sun ce komai a kan abinda kuke so. Takaitaccen bayani ne wanda zaku iya fahimta da kanku. Kun bukaci rahoto kuma kun bada lokacin da kuke son samun shi.

"Za ku iya tunawa cewa shugaban sojin kasa ya karba ragamar mulkin kasa da watanni biyu da suka gabata.

“Lokacin da kuka bukaci wannan rahoton aka yi amfani dashi wurin tattara shi yadda za a iya ganewa.

“Maganar kudin makami da kuke bukatar sanin inda suke ya dace ne ku tambaya wasu. Zan ce gara ku kira wadanda kuka san suke da bayanin rahoton nan," shugaban sojin ga 'yan majalisar.

Wani dan kwamitin daga jihar Delta, Ejiro Ogene, tun farko ya nuna fushinsa ga COAS din a kan kin bayyana gaban kwamitin.

KU KARANTA: Ba a zabe ni domin biyan albashin ma'aikata ba, Gwamna El-Rufai

Kamar yadda yace, majalisar tarayya ita ce gidan 'yan Najeriya kuma kowa da ke aiki na gwamnati a kasar nan yana yi wa 'yan Najeriya ne.

"Da muka bukaci zuwanka, jama'a ne ke magana, fifiko kuwa yana ga jama'a ne. Idan muka dube shi a haka, abubuwa za su sauya.

"Ina jiran ban hakuri daga COAS ba bayani ba. Jama'a kake bautawa kuma sune suka dauke ka aiki," yace.

A wani labari na daban, yayin da kasar Saudi Arabia ta sanar da cewa ba a samu ganin watan Ramadan ba ranar Lahadi, Mai alfarma Sarkin Musulmi ya bukaci 'yan Najeriya su fara duban jinjirin watan Ramadan a ranar Litinin.

Wannan lamarin ya janyo cece-kuce daga jama'a da dama, sai dai Legit.ng ta samu zantawa da Shehin Malami Ustaz Abu Jabir wanda aka fi sani da PenAbdul.

Asali: Legit.ng

Online view pixel