Da duminsa: 'Yan ta'adda na shirin kaiwa filayen jiragen sama farmaki, FG

Da duminsa: 'Yan ta'adda na shirin kaiwa filayen jiragen sama farmaki, FG

- FAAN tace ta samu labarin harin da ake shirin kaiwa tashoshin jiragen sama dake kasar nan daga ma'aikatar sufurin jiragen sama

- Kamar yadda takardar wacce FAAN ta gabatar ga shugabannin jami'an tsaron tashoshin jirgin sama an bayyana sunayen tashoshin

- Takardar ta ranar 9 ga watan Afirilun 2021, ana zargin zasu kai harin tashoshin da suke Kaduna, Maiduguri, Sokoto, Kano, Abuja da Legas

Hukumar tashoshin jiragen saman Najeriya (FAAN) ta ce ta samu labari daga ma'aikatar sufurin jiragen sama akan yunkurin harin da ake shirin kaiwa filayen jiragen sama da suke fadin kasar nan.

FAAN ta gabatar wa da shugabannin tsaron tashoshin jiragen sama wannan sanarwar.

Kamar yadda takardar wacce TheCable ta gani ta ranar 9 ga watan Afirilun 2021, za a kai hari tashoshin jiragen sama da suke Kaduna, Maiduguri, Sokoto, Kano, Abuja da Legas.

An baiwa shugabannin tsaron tashoshin jiragen saman umarnin bayyana hanyoyi da dabarun kariya daga harin sannan an nemi su yi zaman gaggawa don samar da yadda za a bullo wa lamarin.

KU KARANTA: Da duminsa: An sheke soji 3 da wasu 'yan ta'adda a harin Boko Haram a Damasak

Da duminsa: 'Yan ta'adda na shirin kaiwa filayen jiragen sama farmaki, FG
Da duminsa: 'Yan ta'adda na shirin kaiwa filayen jiragen sama farmaki, FG
Asali: Original

KU KARANTA: Boko Haram sun kai hari ma'adanar kayan tallafi, sun kone wurare a Borno

Karin bayani na nan tafe...

A wani labari na daban, Rochas Okorocha, tsohon gwamnan jihar Imo ya ce zanga-zangar EndSARS ta zalincin 'yan sanda, Boko Haram da sauran matsalolin tsaro suna aukuwa ne sakamakon fatara da rashin adalci.

Yayin da Rochas yake amsar jinjinar "Abokin mutanen Ibadan na musamman" da CCII suka gabatar masa a ranar Asabar ya bayyana hakan.

Jinjinar da Saliu Adetunji, Olubadan na Ibadan ya baiwa Rochas bisa kula da kokarinsa na tallafawa ilimin yaran talakawa da marayu a shirinsa na bayar da ilimi kyauta a makarantun Ibadan, jihar Oyo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng