Fara azumin kafin sanarwan Sarkin Musulmi sabawa Manzon Allah ne, Ustaz Abu Jabir

Fara azumin kafin sanarwan Sarkin Musulmi sabawa Manzon Allah ne, Ustaz Abu Jabir

- A ranar Lahadi ne kasar Saudi Arabia ta sanar da cewa bata ga jinjirin watan Ramadan ba amma za ta cigaba da nema

- Kasar Najeriya kuwa sai ranar Litinin aka fara nema inda ake sa ran ganin shi ko kuma watan ya cika 30 a tashi da azumi a ranar Laraba

- Ustaz Abu Jabir ya tabbatar da cewa duk wanda ya tsallake umarnin Sarkin Musulmi ya dauka azumi, ya sabawa Manzo Allah

Yayin da kasar Saudi Arabia ta sanar da cewa ba a samu ganin watan Ramadan ba ranar Lahadi, Mai alfarma Sarkin Musulmi ya bukaci 'yan Najeriya su fara duban jinjirin watan Ramadan a ranar Litinin.

Wannan lamarin ya janyo cece-kuce daga jama'a da dama, sai dai Legit.ng ta samu zantawa da Shehin Malami Ustaz Abu Jabir wanda aka fi sani da PenAbdul.

Malamin ya bayyana cewa kasar nan tana la'akari da ganin watanmu ne ba kasar Saudia ba. Koda kasar Saudi Arabia tace bata ga wata ba, Najeriya za ta duba watan, idan duk ba a gani ba, toh an yi tarayya a rashin ganin watan.

KU KARANTA: Bayan dadewa babu duriyar Mamman Daura, ya je ta'aziyya Adamawa

Fara azumin kafin sanarwan Sarkin Musulmi sabawa Manzon Allah ne, Ustaz Abu Jabir
Fara azumin kafin sanarwan Sarkin Musulmi sabawa Manzon Allah ne, Ustaz Abu Jabir
Asali: Original

KU KARANTA: Kwankwaso ya bar hakkin sama da biliyan 50 na masu kwagilar tituna, Ganduje

"Duk da kasar Saudia tace bata ga wata ba a ranar Lahadi, dama Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya bukaci a fara duban watan a ranar Litinin wanda shine 29 ga watan Sha'aban. Ana iya ganin shi ranar Litinin ko kuma watan ya cika har 30, sai a tashida azumi Laraba," Malamin yace.

A yayin da Legit.ng ta tambaya malamin a kan hukuncin wadanda suka ce ba zasu saurari mai alfarma Sarkin Musulmi ba, za su fara azuminsu. Sai yace:

"Sun sabawa umarnin Annabi Muhammadu SAW. An san duk inda musulmi suke da bin umarnin Annabi kuma wannan al'amari na hadin kan Musulmi ne. Hatta Sahabbai kan samu ra'ayi wanda ya sha banban da na dukkan al'umma, su kan hakura domin hadin kai.

"Lallai duk wanda yace zai bijirewa umarnin mai alfarma Sarkin Musulmi, tabbas ya sabawa umarnin Annabi Muhammadu SAW."

A wani labari na daban, Rochas Okorocha, tsohon gwamnan jihar Imo ya ce zanga-zangar EndSARS ta zalincin 'yan sanda, Boko Haram da sauran matsalolin tsaro suna aukuwa ne sakamakon fatara da rashin adalci.

Yayin da Rochas yake amsar jinjinar "Abokin mutanen Ibadan na musamman" da CCII suka gabatar masa a ranar Asabar ya bayyana hakan.

Jinjinar da Saliu Adetunji, Olubadan na Ibadan ya baiwa Rochas bisa kula da kokarinsa na tallafawa ilimin yaran talakawa da marayu a shirinsa na bayar da ilimi kyauta a makarantun Ibadan, jihar Oyo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel